Daga Muhammad Awwal Umar, Minna
An bada tabbacin kafin cikar wa’adin mulkin nan na Shugaban Kasa Muhammadu Buhari jama’ar Nijeriya za su tabbatar da canjin nan da suka zaba. Mataimakin Sakataren jam’iyyar APC ta jihar Neja, Alhaji Audu Ibrahim ne ya bada tabbacin hakan a sakatariyar jam’iyyar lokacin da yake zantawa da manema labarai.
Alhaji Audun ya ci gaba da cewa ko a jiharsa ya tsaya ya na da abin nunawa jama’a musamman kan tsaro da ayyukan da suka shafi talakawa, domin kusan dukkanin karkarun jihar babu inda gwamna bai taba ba, musamman samar da wadataccen tubalin tsarin ilimin kimiyya da hanyoyi da kuma tsarin kiwon lafiya a jihar.
“A lokutan baya, muna kokawa akan matsin tattalin arziki da yayi mana dabaibayi, Allah cikin ikonsa da mai girma Shugaban Kasa ya tashi tsaye akan noma da hako ma’adinan kasa kowa ya ga inda aka dosa yanzu, ina da tabbacin jam’iyya za ta yi tsayin daka akan gwamnoni da shugabannin kananan hukumomi wajen ganin an ci gaba da bullo da hanyoyin da zasu amfani talaka.
“Tafiyar APC ba kamar tafiyar gwamnatocin baya ba ne, inda jama’a kan yi ruf da ciki da dukiyar jama’a a kyale su, mu kan a tafiyarmu babu raba in raba da dukiyar jama’a shi yasa muka tabbatar da cewar idanun jama’a ya bude wajen sanya ido akan duk wani abu da zai shigo aljihun gwamnati da yadda za a kashe shi, don haka duk wanda aka samu da kunbiya-kunbiya da kudin jama’a lallai jam’iyya za tai tsayin daka wajen ganin an fito da shi a hukunta shi.
“Ina da tabbacin wannan sabon zubin na shugabancin kananan hukumomi (ALGON) ba za su yi kasa a gwiwa ba wajen goya ma duk shugaban karamar hukumar da aka samu da kokarin awon gaba da dukiyar Jama’a, lallai za su tabbatar da duk hanyoyin da za a bi wajen hukunta shi an yi hakan. Dan haka ina kira da babban murya akan shugabannin kananan hukumomi da su kara zage damtse wajen ganin jam’iyyar nan ta APC ta ba mara da kunya, domin dukkanmu amana ne ga jama’a kuma zamu tabbatar mun bi kowacce hanya wajen kare amanar dukiyar jama’a.”In ji shi