Rabiu Ali Indabawa" />

Ba Ka Cancanci Kujerar Gwamna Ba – Akeredolu Ga Gwamnan Bauchi

Gwamnan Jihar Ondo ya caccaki gwamnan Jihar Bauchi sakamakon goyon bayan makiyaya, yayin da ya ce ya bayyana goyon bayan rike bindiga ga makiyaya a matsayin tunzurawa kan aikata ta’addanci.

Ya kuma bayyana cewa, masu hali irin na gwamnan ba su cancanci aikin gwamnati ba, saboda ya  bayyana goyon bayansa ga makiyaya, wadanda ke dauke da bindigogin AK-47.

Gwamnan Jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed, ya fuskanci shan suka daga mutane ta kowane bangarorin siyasa wadanda suka bayyana kalaman nasa da “a matsayin rashin kulawa da kuma tunzura jama’a.”

Mohammed ya ba da hujjarsa ta cewa su mallaki bindigogi, inda ya bayyana nufinsa cewa, hakan zai zama suna cikin shiri domin kare kai daga barayin shanu da sauran barazana, kamar yadda jaridar Nigerian Tribune ta ruwaito.

Shugaban kungiyar gwamnonin Kudu maso Yamma kuma gwamnan Jihar Ondo, Mista Rotimi Akeredolu, ya bayyana gwamnan na Bauchi a matsayin mai tayar da hankali kuma wanda bai cancanci mukamin gwamnati ba.

Da yake magana ta bakin Kwamishinansa na yada labarai da wayar da kai, Mista Donald Ojogo, Akeredolu ya nuna takaicinsa kan kalaman da aka jingina ga gwamnan Bauchi, yana mai bayyana shi a matsayin abin ban tsoro da takaici. Gwamnan ya ce yana da yakinin cewa gwamnan bai fadi wadancan kalamai ba, idan kuma ya tabbata ya fadi haka, a cewarsa hakan nufin cewa, “Gwamnan Jihar Bauchi ya ayyana a madadin Gwamnatin Tarayya, Dokar Zartarwa wanda a yanzu ta ba dukkan ‘yan Nijeriya, makiyaya baki daya damar daukar haramtattun bindigogi don kare kai. ”Wannan shi ne ainihin abin da Gwamnan ya yi kuma ya nuna ta hanyar halayensa wanda ke nuna cewa ko wasu ‘yan Nijeriya suna so ko ba sa so, makiyaya dole ne su dauki AK-47 don kare kansu.” in ji Akeredolu.

Gwamnan, wanda ya kuma bayyana bayanin a matsayin magana mara ma’ana da tunzura mutane. “Gwamnan Bauchi ya nuna halayyarsa da dabi’unsa ya kai mu mataki na gaba kan turbar rashin tsari. Bai cancanci mukamin gwamnati ba, mutanen masu irin wannan hali ba su dace da aikin gwamnati ba,” inji shi.

 

Exit mobile version