Kamar dai yadda aka yi tunani, shirin Majalisar Kasa na haramta wa Kungiyoyi Kadago na bangaren Lafiya na cigaba da fuskantar ce-ce[1]kuce daga Kungiyar Kwadago (NLC) da sauran kungiyoyin dake karkashinta, musamma kungiyar Likitoci ta Kasa NARD.
Tuni dai dokar da ake neman a yi wa sashi na Cap T 8 na dokokin warware rikici da matsalolin da ya shafi kungiyoyin kwadago na Tarayyar Nijeriya na shekarar 2004 ta samu tsallake mataki na farko a majalisar wakilai na tarayya. Dokar ta shirya haramta wa ma’aikatan lafiya a matakin gwamnatn tarayya, gwamnatin jiha da kuma kananan hukumomi shiga duk wani na’uai na yajin aiki.
Dan majaisar wakilai mai wakiltar mazabar Igboeze North/Udenu, a Jihar Inugu, Simon Atigwe, ya gabatar wa da majalisar daftarin kudurin dokar, ta kuma tanadi da a gaggauata zartar da hukunci a kan dukkan matsalolin da suka taso a tsakanin gwamnati da ma’aikatan lafiya da kuma ma’aikata da ke gudanar da ayyuaka masu muhimmanci a kasar nan.
A martaninsa a kan dokar, Shugaban Kungiyar Kwadago (NLC), Ayuba Wabba, ya bayyana cewa, wannan abin dariya ne, hakan kuma yana nuna cewa, ‘yan majalisar basu da masaniya a kan yadda ake gudanar da harkokin kugiyoyin kwadago a sassan duniya kamar yadda Kungiyar Kwadago ta Duniya (ILO) ta tanada.
Shugaban kwadagon ya kuma kara da cewa, sashi na 751 na dokokin kungiyar kwadago ta duniya ta tanadar wa ma’aikata a dukkan bangarori su yi amfani da dukkan mataki da ya dace wajen kare hakkokin su, haka kuma sashi na 42 na kundin dokokin Nijeriya na shekarar 1999 ya haramta a nuna wa dukkan kungiyoyin kwadago banbanci kowanne iri. Saboda haka haramta yajin aiki ya ci karo da wannan sashi na dokar da ake neman kirkirowa.
Duk da mun amincewa da cewa, dole a kawo karshen yawaitar yajin aiki musamman a bangaren ma’aikatan lafiya, amma kuma bamu amince da shirin samar da dokar haramta shiga yajin aiki ba don yin haka tamkar shiga hakkin ma’aikatan ne wadda doka ta basu.
Maimakon shirya dokar hana ma’aikatan lafiya shiga yajin aiki, musamman ganin ma’aikatan na shiga yajin aikin ne don tursasa wa hukumomi biyan wa musu bukatun su ne, ya kamata majalisar kasa ta mayar da hankali wajen ganin an kawo karshen matsalolin da ke haifar da yajin aiki a tsakanin kungiyoyin kwadago a kasar nan.
A hakikanin gaskiya, ma’aikata na shiga yajin aiki ne bayan sun bi duk wata hanyar neman biyan bukatunsu wadanda suka hada da tattauanwa, bayanin ya nuna cewa, ma’aikata na shiga yajin aiki ne a matsayin mataki na karshe na ganin gwamnati ta cika bangarenta na yarjejeniyar da ta dauka tsakaninta da kungiyoyin ma’aikatan. Wai shin ‘yan majalisar sun taba tambayar mai ya sa daraja bangaren lafiya a Nijeriya a matakin awo na duniya yake a 187 daga cikin 191? In har basu sani ba, to yakamata su fahimci bangaren lafiya a Nijeriya na tsananin bukatar tallafi don inganta shi ya kai ga matakin yadda ake gudanar da al’amurra a fadin duniya.
A bin da ake bukata a halin yanzu shi ne, samar da kudade da kayan aikin da ake bukata a bangaren lafiya, in har an samar da wadannan to, tabbas lamarin yajin aki zai zama tarihi a kasa nan. Babban abin da kasar nan ke bukata a halin yanzu shi ne yadda majalisa za ta tursasa wa masu rike da madafun iko a kasar nan su rika amfani da cibiyoyin lafiya na gwamnati, wanda ake yin watsi da su saboda ba su da kayan aiki na zamani.
Tattauna kudurin dokar na nuna kamar ‘yan majalisar na nuna cewa, kamar ma’aikatan na jin dadin shiga yajin aiki ne, ko kuma dalilan da ma’aikatan ke bayarwa na shiga yajin akin basu da kwari ne. Ya kamata ‘yan majalisar su tambayi kansu, ko mai yasa dubban ma’aikatan lafiya ke fita kasashe duniya don neman aiki mai tsoka?
Tabbas baban dalilin yawaitar yajin aiki a kasar nan shi ne yadda aka yi watsi da bangaren ba tare da kulawar da yakamata ba. Wannan jaridar na kallon shirin samar da dokar a matsayin wani hanyar dankwafar da ma’aikatan tare da hana su neman hakkinsu duk kuwa da cewa, dokar kasa ta basu damar neman hakkin su.
A kan haka muke kira ga ‘yan majalisa da su yi watsi da shirin dokar, inda kuma sun ki yin haka muna kira ga Kungiyar Kwadago ta Kasa NLC da sauran gamayyar kungiyoyin kwadago su yi amfani da dukkan matakin da doka ta amince musu wajen ilimantar da ‘yan majalisar tare da taka musu birki kan wannan shiri nasu ba tare da bata lokaci ba.