Ba Ma Goyon Bayan Sabuwar Zanga-Zangar Sowore – ’Yan Zanga-zangar EndSARS

Daga Abubakar Abba

 

Ma su zanga-zangar a rusa jami’an ’yan sanda EndSARS na ainihi sun bara, inda su ka zargi mai kafar yada labarai ta yanar Gizo ta SaharaReporters, Mista Omoyele Sowore, bisa yunkurin sayen wasu kungiyoyin da ke yin zanga-zangar don kawai ya cimma wani burin sa.

Sun yi zargin ne a cikin sanarwar da Dakta Orji Nwakocha daga Kudu Maso Yamma da Dakta Aremu Babatunde daga Kudu Maso Gabas, Kwamaade Frank Jaja daga Kudu Maso Kudu, Alhaji Ibrahim Dan Iya daga Arewa Maso Yamma Sheik Mohammed Adamu daga Arewa Maso Gabas, Mista Dakwohi Samson daga Abuja da kuma Kwamarade Peter Yohana daga Arewa ta Tsakiya su ka sanya wa hannu su ka kuma bai wa LEADERSHIP A Yau a Kaduna.

Sun kuma zargi Sowore bisa yunkurin cin zarafin Gwamnatin Shugaban kasa Muhammadu Buhari, inda su ka buga misali da zanga-zangar da a ka yi a Abuja a ranar daya a watan Nuwambar 2020, inda yan kalilan na ma su zanga-zangar aka gani su na ci gaba da zanga-zangar.

A cewarsu, hakan ya nuna cewa, wata manufa ce ta Sowore don ya cimma burin sa na kara rura wutar zanga-zangar da tuni aka dakatar a kasa baki daya.

Bugu da kari, sun yi nuni da cewa, ganin yadda Sowore ke kan gaba a zanga-zangar a filin tashi da saukar jirage na kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da a shalkwatar tsaro yan sanda, inda ma su zanga-zangar su ka bar Allunan zanga-zangar a rusa SARS akan tituna, hakan ya batawa ma su zanga-zangar na ainahi rai, inda su ka yi kira ga daukacin matasan kasar, su yi watsi da sabuwar zanga-zangar ta Sowore.

A cewarsu, ganin cewa, Sowore ya gaza cimma kudirin sa na a yi wa gwamnatin Buhari bore kuma ya san ba zai iya samun mubiya ba amma ya ke son fakewa da zanga-zangar, ya za ma wajibi a kaurace ma sa.

Sun yi nuni da cewa, a yanzu haka, Omoyele Sowore ya na fuskantar tuhuma a gaban Kotu bisa zargin sa tun a 2019 na jagorantar ayi wa gwamnatin shugaba Muhammadu Buhari bore, inda hakan ya janyo aka kama shi ake kuma ci gaba da shari’a bisa zargin sa kan manyan laifuka bakwai da su ka hada da safafar kudi da sauran su a gaban babbar Kotun da ke Abuja.

A saboda hakan, mu na son mu sanar da duniya cewa, mun nesata kan mu daga Sowore da yan kanzagin sa kan sake kaddamar da sabuwar zanga-zangar a rusa jami’an ’yan sanda na EndSARS wacce tu ni, aka tsayar da ta ainihin don jiran matakan da gwamnatoci a kasar nan za su dauka.

Sun yi nuni da cewa, ganin yadda zanga-zangar ta baya wa su ’yan daba su ka mamaye ta, inda hakan ya janyo mutuwar wa su, sa ce-sa ce da kone-kone, ba bu wani dan kasar mai kishi da zai so a sa ke mai-mai ta ta.

“Mu na kira ga miliyoyin ma su akida irin ta mu, musamman matasan da ke a jihohi 36 na kasar nan da na Abuja su nesanta kan su daga sabuwar zanga-zangar ta Sowore domin kuwa babbar baraza na ce ga zaman lafiya da kuma tattalin arzikin kasar nan, musamman ganin kasar ba ta gama fita daga nakasun da annobar Korona ta yi wa tattakin arikin kasar ba.”

Exit mobile version