Daga Umar Faruk, Birnin-Kebbi
Kungiyar Kwadago ta Kasa (NLC) reshin Jihar Kebbi a jiya ta gudanar da zanga-zangar lumana, don nuna rashin amincewarta ga yunkurin cire tsarin biyan mafi karancin albashin ma’aikata daga cikin Kundin Dokokin Nijeriya da wani dan Majalisar Dokokin Tarayya, Hon. Garba Datti, ya ke neman mambobbin majalisar su amince da kudirin, don bai wa jihohin kasar damar kayyade albashinsu.
Kungiyoyin ta Kebbi sun fito ne, domin yin tattaki a kafa tun daga bakin babban ofishin kungiyar Kwadago ta Jihar dake a kan titin tsohon gidan waya, wato NITEL, a cikin Babban Birnin Jihar, Birnin Kebbi har zuwa bakin harabar Majalisar Dokokin Jihar Kebbi, wanda ya kai kimanin tafiyar kilomita uku, don kawai bayyana wa mambobbin majalisar rashin amincewarsu ga irin yunkurin da Majalisar Dokoki ta Tarayya ta soma gabatarwa.
Bisa ga hakan ne shuwagabannin Kungiyar Kwadago da sauran na wasu kungiyoyin suke nuna rashin amincewarsu ta hanyar gudanar da zanga-zangar lumana da kuma bada takarda a rubuce ga Majalisar Jihar.
Haka zalika, sun kara bayyana cewa, ya zama wajibi ga Majalisar Dokoki ta Jihar ta amince da bai wa bangaren gidan shari’a cin gashin kanta, sai kuma su tabbatar da sun shigo, don magance matsalar hauhawar farashin man fetur, musamman a Jihar Kebbi inda manoma ke yawan amfani da man fetur wurin ban-ruwan amfanin gona da suke nomawa.
Shugaban NLC na Jihar ,Kebbi Umar Haladu Alhassan, nan take ya isar da sakon uwar kungiyar ta kasa ga majalisar jihar.
A nashi jawabi, Kakakin Majalisar Dokoki na Jihar Kebbi, Rt. Hon. Samaila Abdulmuminu Kamba, wanda mataimakinsa Muhammad Buhari Aliero ya wakilta yayin karbar tawagar, ya ce, “muna ba ku tabbacin cewa, wannan yunkurin daga Majalisar Dokoki ta kasa yake, ba za a taba zartar da shi ba tare da amincewar Majalisun Dokokin Jahohi 36 na kasar nan ba.
“Sobada haka idan aka aiko wa Majalisar Dokoki ta Jihar Kebbi, ba za mu kaddamar da ita ba har sai mun kira taron masu ruwa da tsaki, don jin ra’ayinku. Haka kuma za mu duba sauran bukatunku, don yi musu adalci. Ina ba ku hakuri kan rashin halartar Kakakin Majalisar, wanda sa’anin aiki ne ya hana shi ganawa da ku.”
Ya kuma yaba wa shuwagabannin wadannan kungiyoyin da suka shirya wannan zanga-zangar ta lumana, don bayyana koken su ba tare da wata matsala ko hatsaniya ba.
Daga karshe kuma Mataimakin Kakakin ya gode wa dukkan mambobbin kungiyoyin kan hada kansu wuri daya, don tabbatar da cewa, wakilan da suka zaba sun yi musu wakilci mai ingance. Ya kuma kara da jan kunnuwansu ga tabbatar da cewa, ba a samu wata hatsaniya ba.