Ba Mu Amshi Sakamakon Warkewar Gwamna Bala Ba, Cewar Gwamnatin Jihar

Kwamitin yaki da cutar numfashi ta Coronavirus a jihar Bauchi ya shaida cewar har zuwa yanzu bai amshi sakamakon da ke tabbatar musu da cewar gwamnan jihar Bala Muhammad ya warke daga cutar ba.

Sai dai kwamitin ya tabbatar da cewar gwamnan yana cikin koshin lafiya kana yana ci gaba da gudanar da harkokinsa ba tare da wata matsala ba a inda yake killace.

Shugaban kwamitin kuma mataimakin gwamnan jihar Sanata Baba Tela shine ya shaida hakan a yau Litinin sa’ilin da ke ganawa da ‘yan jarida a gidan gwamnatin jihar.

Ya ce, gwamnan a kwana-kwanan nan yayi ganawa ma ta kafar sadarwa na Skype kuma babu wani alamin damuwa a jikinsa, inda ya ce ko a jiya gwamnan yayi ganawa da kungiyar gwamnonin Nijeriya garau dinsa.

“Tsarin shine idan idan an dauki samfurin mutum za a jira sakamakon gwajin nasa. Ba za mu dogara da abun da muke ji ba, ko abin da muke gani a kafafen sadarwar zamani ba. Ko kuma daga wajen dan rahoton jaridar DailyNigeria ba. Za mu dogara ne kawai da abin da NCDC ta bamu. Sun dauki samfuri mu kuma muna jiran sakamakon gwajin daga garesu; muddin sakamakon gwajin bai zo ba, a matsayinmu na gwamnati ba za mu bayyana ra’ayinmu a kai ba,”

Ya kara da cewa har zuwa yanzu suna jiran sakamakon daga hukumar dakile yaduwar cutuka ta kasa NCDC domin ta tabbatar musu da sabon gwajin da aka yi wa gwamna Bala, “Da zarar sakamakon gwajin ya zo daga NCDC za mu bayyana ra’ayinmu a kai. Muna ci gaba da jiran sakamakon gwajin har yanzu.

Idan za ku iya tunawa dai wata kafar sadarwa ta yanar gizo ta bada labari a makon jiya da take cewa gwamnan ya warke daga cutar ta Koronabairus.

Sanata Baba Tela ya sake jaddada cewar gwamnan yana cikin koshin lafiya ba tare da nuna wata alamar damuwa a jikinsa ba, sai yake mai tabbatar da cewar daga lokacin da suka samu sakamakon daga hannun hukumar NCDC za su shaida wa jama’a.

Ya kuma shaida cewar suna ci gaba da yin duk mai iyuwa domin tabbatar da dakile yaduwar cutar a jihar.

A gefe guda kuma ya sanar da cewar jihar za ta kafa cibiyar gwajin masu dauke da cutar nan ba da jimawa ba.

Exit mobile version