Ba Mu Bukatar Sauya Shekar Gwamnan Bauchi Zuwa APC, In Ji Wata Kungiya

Makarantu

Daga Khalid Idris Doya,

Wata kungiyar siyasa ta magoya bayan APC a Jihar Bauchi mai suna ‘Manazarta Siyasar Jam’iyyar APC’ ta bayyana cewar jita-jitan da ake ta yadawa na cewar Gwamnan Bauchi, Sanata Bala Muhammad zai sauya sheka daga jam’iyyar PDP zuwa APC zancen kanzon kurege ne kawai, kuma ma sam basu bukatar hakan.

Kungiyar tana cewa ba su bukatar gwamnan ya shigo musu jam’iyya kuma ma zamansa a PDP dinsa ya fi masa alfanu ta kowace fuska, amma wasu na ta yada jita-jitan da babu tushe.

Shugaban kungiyar, Yahaya Idris Sulaiman, shi ne ya shaida hakan a hirarsa da ‘yan jarida a ranar Litinin, yana mai cewa su kam sam ba su bukatar gwamnan ya koma cikin APC domin rashin nagartarsa a garesu.

“Muna kira ga jama’an Jihar Bauchi da su kwantar da hankulansu jita-jitan da ake yadawa a kafafen sadarwar zamani da gidan rediyo ba gaskiya bane na cewa gwamnan Jihar Bauchi Bala Muhammad zai koma cikin jam’iyyar APC. Za mu tabbatar bai samu kofar shiga ba.

“Za mu cigaba da tafiya da mutanen kwarai da kirki a jam’iyyarmu ta APC ba za mu bari wasu marasa gaskiya su shigo mana ba.

“Muna baiwa gwamna Bala Muhammad shawarar ya yi zamansa a jam’iyyar da ya ke yi da har wasu ke kallon kamar yana aiki ne,”

“Eh, gwamnan na kokarin sauya sheka. Amma da izinin Allah hakan ba zai faru ba. Yayi zamansa kawai jam’iyyar da ta bashi dama.

“Idan yana tunanin yanayin mai kyau, don meye ba zai yi zamansa a inda yake ya sake neman tazarce ba? A bincikenmu bai yin abun da ya dace illa ma tulin basuka da yake lafta wa jihar Bauchi.”

Daga bisani kungiyar ta jinjina wa shugaban kasa Muhammadu Buhari a bisa ayyukan titina, layukan dogowa da yake yi tun daga jihar Katsina zuwa jamhuriyar Nijar, da gina hanyar Akwanga a Nasarawa zuwa Jos da Bauchi, daga Bauchi zuwa Adamawa da kuma gina gadoji na zamani a yankin Arewa da ma kudanci.

Kungiyar ta jinjina wa kokarin da gwamnatin Buhari ke yi wajen shawo kan matsalar tsaro da ya addabi kasar nan, kungiyar tana mai cewa ana samun cigaba a halin yanzu.

Exit mobile version