Abba Ibrahim Wada" />

Ba Mu Da Isassun ’Yan Wasan Da Za Mu Buga Wasanninmu Na Gaba – Klopp

klopp

Mai horar da ‘yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Liverpool, Jurgen Klopp ya ce bashi da wadattun ‘yan wasan da zai yi amfani da su wajen sauye-sauye bayan karawar tawagarsa da kungiyar Ajad a ranar Talata, dai dai lokacin da bayanai ke nuna cewa Thiago Alcantara zai kai badi, wato sabuwar shekara gabanin ya kammala murmurewa daga raunin da ya samu a gwiwa.

Jurgen Klopp ya sake samun karin majinyata ne bayan raunin James Milner a karawar Liverpool da Brighton ranar asabar din da ta gabata, wasan da suka yi canjaras 1-1, inda Milner ya samu rauni a kafada.

A cewar Klopp damuwarsa ba wai gasar ta cin kofin zakarun Turai ba, babbar damuwarsa halin da ‘yan wasan za su shiga saboda babu masu sauyarsu a fili kuma ga wasanni suna tunkarar kungiyar a nan gaba kadan masu yawa.

Mai horar da kungiyar ta Liverpool ya ce alfarmar da ya kamata ayi musu ba wai iya tawagarsa ba hatta sauran kungiyoyi da ke fuskantar yawan majinyata shi ne sauya jadawalin wasanninsu don bai wa ‘yan wasa cikakken hutu.

Rabon Alcantara da buga wasa dai tun bayan canjaras din Liverpool da Eberton ranar 17 ga watan Oktoba wanda ke matsayin kari kan ‘yan wasa irinsu Kaftin din tawagar wato Jordan Henderson da Birgil Ban Dijk da Joe Gomez da kuma James milner baya ga Dherdan Shakiri da Trent Aledandre-Arnold da kuma Naby Keita dukkanninsu da ke ci gaba da jinya ba kuma tare da yiwuwar dawowarsu kafin sabuwar shekara ba.

Tuni dai Klopp da mai koyar da ‘yan wasan Manchester City Pep Guardiola suka nemi a bawa kungiyoyin damar canja ‘yan wasa biyar a gasar firimiya kamar yadda aka bayar da damar a kofin zakarun turai

Exit mobile version