Nasir S Gwangwazo" />

Ba Mu Da Niyyar Addabar Ma’aikatan Kano Idan Mun Kafa Gwamnati – Kwankwaso

Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya karyata dukkan rahotannin da ke nuni da cewa, PDP za ta addabi ma’aikatan gwamnati a jihar Kano, idan ta kafa gwamnati a zaben da ke tafe, ya na mai cewa, tsabar karairayi ne kawai irin wadannan bayanai marasa kan gado a gari.

Sanata Kwankwaso ya bayyana a hakan ne a wata sanarwa da ya bayar ta hannun mai magana da yawunsa, Hajiya Binta Spikin, a yayin da tsohon gwamnan ya ke mayar da martani kan rahotannin da wasu kafafen yada labarai su ka ruwaito cewa, Kwankwason zai umarci dan takarar jam’iyyar PDP, Injiya Abba Kabir Yusuf, ya kori dukkan ma’aikatan da gwamnati mai ci a karkashin jagorancin Injiniya Abdullahi Umar Ganduje na jam’iyyar APC.

Ya ce, “abin takaici ne cewa wasu kafafen yada labarai su na bayar da labaran karya masu taba zuciya. Wannan ya hada da rubutun da a ka dauki nauyi a jaridar Daily Times cewa wai Sanata Kwankwaso zai rage ma’aikata idan a ka zabi Injiniya Abba Kabir Yusuf a matsayin gwamna da kuma mummunan rubutun da a ka yi a Sahara Reporters da ke yanar gizo a na zargin Sanata Kwankwaso da bai wa Abba Kabir Yusuf umarnin kada ya biya mafi karancin albashi na Naira 30,000 idan an zabe shi.

“Irin wadannan labaran karya an kirkire su ne da gangan da nufin a karya ma na gwiwa a yayin da mu ke jiran karatowar zaben cike gurbi a Kano,” in ji sanarwar, ta na mai kara wa da cewa, “mu masu jan hankalin mutane da cewa, Sanata Kwankwaso ba zai taba zama mai akidar korar mutane daga aiki ba ballantana kuma Injiniya Kabir Abba Yusuf.”

Spikin ta kara da cewa, tunda mutanen jihar Kano sun nuna ga abinda su ke so, to ya kamata a ba su, maimakon a koma gefe a na kirkirar jita-jita maras tushe.

Exit mobile version