‘Ba Mu Da Yunwar Cin Ƙwallaye Yanzu’

Mai koyar da ‘yan wasan Chelsea, Antonio Conte ya ce ya kamata ƙungiyarsa ta dawo da ƙishirwar cin ƙwallaye, bayan da AS Roma ta doke ta da ci 3-0 a gasar cin kofin Zakarun Turai a ranar Talata.

Cikin ƙwallo ukun da Roma ta ci Chelsea, Stephan El Shaarawy ne ya ci biyu, kuma hakan ya sa ƙungiyar ta Chelsea ta koma ta biyu a kan teburin rukuni na uku.

Chelsea za ta kai wasan zagaye na biyu idan har ta doke Ƙarabang a wasan gaba da za ta buga a gasar ta Zakarun Turai a tsakiyar wannan watan da muke ciki.

Conte ya ce duk wata babbar ƙungiya ya kamata ta samu natsuwa da juriya da haɗin kai a koda yaushe idan har tana buƙatar nasara a wasanninta.

Conte ɗan ƙasar Italiya ya lashe kofin Firimiya na bara a kakar farko da ya ja ragamar ƙungiyar, kuma wasa biyar aka doke shi cikin 38 da ya buga.

Chelsea wacce ta yi rashin nasara a wasa uku daga 10 da ta yi a Firimiyar, za ta karɓi bakuncin Manchester United a ranar Lahadi a filin wasa na Stamford Bridge dake birnin Landan.

Mai tsaron ragar ƙungiyar Thiabau Courtois ya ce dole sai ‘yan wasan ƙungiyar sun doke United idan har suna son su cigaba da zama a cikin ƙungiyoyin da za su iya lashe kofin Firimiya na bana.

Exit mobile version