Daga, Sharfaddeen Sidi Umar,
Shugaban darikar Tijjaniyya na duniya bakidaya, Sheikh Mahi Nyass ya musanta nada Mai Martaba tsohon Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II a matsayin shugaban Darikar a Nijeriya.
Nyass wanda shine dan Shehu Ibrahim Nyass, jagoran jaddada darikar Tijjaniyya ya bayyana hakan a tattaunawarsa da manema labarai a Sakkwato a ranar Litinin.
Ya ce nada Khalifan Darikar Tijjaniyya a Nijeriya da Afrika lamari ne na gabatar da wadanda ke bukata da tantancewa daga manyan Malamai a Nijeriya da Senegal.
“Ba a riga an tattauna wannan matsayar ba a kowanne irin waje, sai an cimma matsaya kafin a bayar da sanarwa. Bayan gabatar da sunan wanda ke nema daga shugabanni wajibi ne a gabatar da, takardar gabatarwa daga rukunin Malamai wadda babban jagoran Tijjaniyya na duniya ya sanyawa hannu kafin nada mutum wannan matsayin.” Nyass ya bayyana.
Ya ce a yanayin da ake ciki a yanzu, tsohon Sarkin Kano, Mai Martaba Sanusi II bai bi wadannan hanyoyin ba, kuma a kashin kansa bai gabatar da kansa ko ya nuna ra’ayin bukatar a nada shi shugabancin Darikar Tijjaniyya na Afrika ba.
Bugu da kari a wata tattaunawa ta daban da manema labarai, Sheik Ibrahim Dahiru- Bauchi, dan fitaccen malamin Addini, Sheikh Dahiru Usman Bauchi ya bayyana yaduwar labarin nada Muhammad Sanusi II a matsayin shugaban Darikar a Nijeriya a matsayin labarin shaci fadi kawai.
Ya ce Darikar Tijjaniyya ta ginu ne a kan ilimi da koyarwar malamai da bin ka’idoji da tsare dokokin Allah. A cewarsa ba a fahimci bayanin da kanen jagoran Tijjaniyya Sheikh Makey ya yi ba a inda ya nuna Sarki Sanusi II ya tako sawun Kakansa, tsohon Sarkin Kano Muhammadu Sanusi I.
Ya jaddada cewar Makiy Nyass ya bayyyana yanayin al’amurran rayuwa kwatankwacin yadda aka cire Sarki Sanusi I a kan mulki shi ma Jikansa Sarki Sanusi II ya fuskaci irin wannan kaddarar a rayuwa.