Ba Mu Saida Kayayyakin Makarantar Sa’adu Zungur –Dakta Mudi

Daga Khalid Idris Doya, Bauchi

A ‘yan kwanakin nan ne wasu iyaye suka rinƙa bayyana damuwarsu a bisa abun da suka ce hukumar gudanarwa na makarantar sakandari Sa’adu Zungur da ke Bauchi suna aikatawa na ɗiban kayyakin makaranta domin saida musamman irin su fefa ɗin fotokofi samfurin A4 inda suka amsa daga hanun ɗalibai a lokacin da suka ci tararsu bayan aikata laifuka ko kuma a lokutan da suke kawowa haɗe da kayan rijista.

Haka masu ƙorafin sun bayyana makarantar tana sanya tara wa ‘ya’yansu domin samun kayyakin da kuma ƙara yawna kuɗin PTA, a maimakon yin amfani da su sai suke saidawa. Iyayen waɗanda suka buƙaci a sakaye sunansu, sai dai ba su yi bayanin a ina ake saidawa ko kuma ma wa ake saidawa ba.

A bisa wannan ƙorafin ne kuma maka garzaya makarantar domin gudanar da bincike, bayan nazartar abubuwan da muka gani, mun kuma zan ta da shugaban wannan makarantar Dakta Mudi Musa Jahun inda ya fara  a bayyana cewar girman makarantar da kuma yawan ɗaliban da makarantar ke da su ne ya sanya suke yawaita samun irin waɗannan ƙorafe-ƙorafen, yana mai cewa zancen suna saida wani abu wannan soki-burutsu ne kawai daga wasu iyayen da suke kawo son zuciya a cikin sha’ainin gudanarwa na makarantar.

Dakta Jahun ya ce, “mafiya yawan iyaye ba su ma san yaya wannan makatantar take ba. akwai wani uba da ya zo ya ce su suna biyan kuɗin PTA ba san me ake yi da su ba, da na tashi da shi muka zaga cikin makarantar nan aka nuna masa yanda ake gudanar da wannan makarantar da kansa ya zo yana bani haƙuri yana cewa kuskuren fahimta ne. malam wannan makarantar ta wuce duk inda kake tsammaninta, domin manyan masu kuɗi suna ciro ‘ya’yansu daga makarantun kuɗi suna kawo su wannan makarantar, waɗanda suke makarantun gwamnati kuma a kowani lokaci burinsu su ga ‘ya’yansu a cikin wannan makarantar ba komai bane illa yanda wannan makarantar take da inganci da kuma nagarta”. Ta bakinsa

Jahun ya ce dukkanin makarantar da babu horo to tabbas ilimi ba zan yi inganci ba “mu a nan yanayin horonmu muna kasashi kashi-kashi ne. babu yanda za a yi a dawo makarantanta a yi sati biyar yaro ya yi sati uku a ciki bai zo ba, ka kirashi ka ce masa ya baka zo makaranta sannunka! Gobe me kake tsammanin zai yi. Mu idan mutum ya yi sati guda bai zo makaranta ba a cikin makaranta muke horas da shi. Idan kuma yaro ya wuce sati ɗaya bai kai sati biyu ba, mukan ba shi takarda ya je ya zo da iyayensa ne. idan kuma ya wuce sati biyu bayan mun bashi takardar dakatarwa sai mu ce masa ya bi ta ma’aikatar ilimi ya bayyana dalilinsa na rashin zuwa makaranta”.

Ya ɗaura da cewa “idan suka dawo mukan ce yaro ya je ya kawo maka ko kuma Rim na A4 saboda gudanar da aiyukan makaranta, wannan ba ƙarya bane muka ƙarɓa domin gudanar da aiyukan makaranta. Dukkanin wanda kuma yake ganin muna tara irin waɗannan abubuwan muna sayarwa dukkaninmu a Bauci muke sai ya zo ya kawo mana shagon da muka taɓa zuwa maka saida kayan makaranta, a nawa muka sayar ko kuma mutum ya zo ya ce mana kun mashi rim guda kaza a hanun yara muna son ku nuna mana me kuka yi da shi”. Ta bakinsa

Sai ya bayyana cewar wallahi hanyoyin da suka ɗauko domin gyaran wannan makaratar ƙorafi ko nuna damuwa daga wasu iyaye masu sanya son zuciya ba zai sanya su daina ba “in ka ga mun daina to sai dai in an ɗaga mu. Yanda muka kawo gyara kuma muna ganin yanda ilimi ke gudanuwa da ci gaba babu wanda ya isa ya canzamu a kan abubuwan da muke yi”. In ji sa

Mudi Jahun ya ce maganar da ake yi na yawaita ƙorafe-ƙorafe kan kuɗin PTA ya ce lamarin duk ba hanya iyayen ma suka ɗauka bane “kuɗin PTA ɗin nan fa 200 kacal a bayan wata uku. Masu cewa muna ƙarɓar kuɗi fiye da haka ba su ma san kuɗin me suke bayarwa ba; ka ga hakan ma sakacin iyaye ne kuɗin rijista ne suke ɗauka kuɗin PTA, kuɗin PTA mu ɗari biyu kaɗai muke amsa”.

Ya ce: “Dukkanin ɗalibanmu sun kai dubu bakwai a wannan makarantar, a cikin fefa mai inganci ake zana jarabawa ga kowani ɗalibi, kuma muna basu sakamakon karatu a dukkanin hotu dukka da A4 muke ammafani. A makarantar nan muna kashe kuɗi wajen biyan albashi waɗanda ba ma’aikatan da gwamnati ta ɗauke su ba sama da dubu 100, don haka mu gorafi bai damunmu kowa ya je ya yi ta yi, amma muna son iyaye suke korafi mai ma’ana”. A cewarsa

Daga bisani ya buƙaci masu ƙorafin da su kasance masu bincike da bin diddigi kafin yanke hukunci yana mai cewa girman makarantar nasu ne ya kawosu ga samun irin waɗannan korafen “ba fa za a taɓa daina ƙorafi a wannan makarantar ba, domin wasu suna yi ne a bisa son rai. An yi jarabawar kammala jiniyo mun yi abun day a dace iyaye sun je suna t ace mun cire ɗalibai mun kaisu wani makaranta alhali kowace makaranta akwai tsarin da ma’aikatar ilimi take tafiya a kai bayan kammala jarabar JCE, wata rana ma iyayen da basu samu an ɗauki ‘ya’yansu ba za ku ji suna bayyana wasu abubuwan fiye da wannan ma”. In ji sa.

Exit mobile version