Kocin Manchester United Jose Mourinho yace baya tunanin kungiyar kwallon kafa ta Manchester city inda yace kungiyoyin da basu samu nasara ba wasanninsu na karshen sati sune a gabansa.
Mourinho ya bayyana hakane bayan da kungiyarsa ta Manchester united ta lallasa Eberton daci 4-0 a ranar lahadi a filin wasa na Old Trafford.
A ranar asabar ne dai Manchester city ta lallasa Watford daci 6-0 har gida wanda hakan yasa kungiyar ta zama ta daya a kan teburin firimiya.
Mourinho ya kara da cewa, baya tunanin Manchester city, domin sun lashe wasansu, abinda yake tunani kawai shine kungiyoyin Tottenham, Asenal, Chelsea da Liberpool wadanda duk basu lashe wasannunsu ba, inda ya bayyana cewa kungiyarsa tasamu dama domin tasamu tazarar maki da kungiyoyin.