Connect with us

LABARAI

Ba Na Nadamar Yin Aiki A Karkashin Jonathan –Namadi Sambo

Published

on

Tsohon mataimakin shugaban kasarnan, Namadi Sambo, ya ce ko kusa ba ya yin nadaman yi wa kasarnann hidima a matsayin mataimakin shugaban kasa a karkashin gwamnatin shugaba Jonathan.

Cikin wata sanarwa da mai taimaka ma gwamnan Jihar ta Bayelsa ta fuskacin manema labarai, Fidelis Soriwei, ya fitar, ya jiwo Namadi Sambo na fadin hakan a ranar Lahadi lokacin da ya kai ziyarar ta’aziyya a garin Toru-Orua, mahaifar Gwamna Seriake Dikson, na Jihar ta Bayelsa, kan rasuwar mahaifiyar gwamnan mai suna, Goldcoast.

Shi ma mai neman tsayawa Jam’iyyar ta PDP takarar neman shugabancin kasarnan, Sanata Dabid Mark, ya kai wa gwamnan na Bayelsa irin wannan ziyarar ta’aziyyar a ranar ta Lahadi.

Namadi Sambo ya ce, yana yi wa Allah godiya da ya ba shi daman zama a mukamin na mataimakin shugaban kasarnan.

Tsohon mataimakin Shugaban kasan, wanda ya ce a kwanan nan ne bankin, Afredim Bank da kungiyar hadin kan Afrika suka nada shi jakada na musamman a wata kasuwar hadin gwiwa a tsakanin kasashe da za ta ci a Cairo, babban birnin kasar Masar. Ya kuma yi kira ga hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta da ta yi abin da ya dace a babban zaben shekarar 2019.

Namadi Sambo ya ce, “Da farko na zo nan ne domin na yi wa dan’uwana da ‘yar’uwata ta’aziyyar rashin Maman mu, na kuma roki Allah da ya ba su hakurin jure wa wannan rashin da aka yi.

“Hakanan kuma muna ta ganin abin da ke faruwa, muna kuma sa ran hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta yi abin da ya dace, muna sa ran za ta gudanar kuma da babban zaben 2019 a cikin adalci da gaskiya.

Namadi Sambo ya yaba wa Gwamna Serieke Dickson, kan iran manyan ayyukan raya kasan da ya gudanar a Jihar ta Bayelsa, musamman yanda ya gina babban filin saukan manyan Jiragen sama masu daukan kaya da na fasinjoji.

“Kai mutum ne wanda a yau kowa ya san shi, musamman a arewacin kasarnan a matsayinka na jagoran samar da hadin kai wanda wannan yana da mahimmanci sosai, kuma ka ci nasarar ganin samar da hadin kan a cikin wannan kasar tamu,” in ji shi.

A na shi bangaren, tsohon shugaban majalisar ta Dattijai, David Mark, wanda ya jagoranci wata kakkarfar tawaga zuwa wajen ta’aziyyar ga gwamnan da jama’arsa, cewa ya yi, Madam Goldcoast ta yi rayuwa mai tsafta ta kuma bar abin koyi a baya.

Daganan ya taya gwamnan da al’ummar Jihar jimamin wannan rashin da aka yi.

Shi ma da yake na shi jawabin, Gwamna Dickson ya bayyana shawarar da iyalan mamaciyar ne suka yanke ta kafa wata cibiya ta wayar da kai ga masu fama da cutar kansa, domin girmama mahaifiyar na su, a karkashin jagorancin gidauniyar, Henry Seriake Dickson Foundation.

Ya kuma yaba ma dukkanin shugabannin da suka kai ma shi ziyarar ta ta’aziyya, wacce ke nu ni da zaman lafiyan da suka yi tare da tsohon Shugaban kasarnan Jonathan a zamanin gwamnatin na shi.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: