Kocin Liverpool, Jurgen Klopp ya ce ba zai karbi aikin horar da tawagar Jamus ba, domin maye gurbin Joachim Low bayan da hukumar kwallon kafar Jamus ta sanar da cewar Low zai ajiye aikin, idan an kammala gasar cin kofin nahiyar Turai ta shekara ta 2021.
Klopp ya ce ba zai zama kocin tawagar Jamus ba, bayan karkare gasar nahiyar Turai inda a cewarsa akwai masu horarwa ‘yan kasar Jamus da yawa kamata ya yi a bai wa wani aikin kasar ba.
Klopp mai shekara 53 a duniya , ya karbi jan ragamar Liverpool a watan Oktoban shekara ta 2015 ya kuma lashe gasar cin kofin zakarun turai ta Champions League a shekarar 2019 da Premier League a kakar 2019 zuwa 2020.
Kofin na Premier shi ne na farko da Liverpool ta lashe a bara da tazarar maki 18 tun bayan shekara 30, amma a bana tana fama da kalubale na rashin nasara wanda shine mafi muni a tarihin kungiyar.
Liverpool wadda ‘yan wasanta da dama suke jinya ta yi rashin nasara a wasa shida a jere a Premier League a bana tana ta takwas a kan teburi sannan Klopp ya ce zai kammala kaka uku ta yarjejeniyarsa a Liverpool da ta rage masa kamar yadda ya yi a Mainz da kuma Borussia Dortmund.
Kocin ya yi wadan nan kalaman ne kafin wasan da Liverpool za ta buga da kungiyar kwallon kafa ta RB Leipzig a gasar cin kofin zakarun turai na Champions League ranar Laraba sai dai a wasan Klopp ya bayyana cewa ‘yan wasansa zasu dage domin samun nasara.
Liverpool ce ta yi nasara a wasan farko da ci 2-0, za su kara fafatawa karo na biyu a Budapest a dai gasar ta zakarun Turai hakan yana nufin duka wasannin guda biyu ba a gidan kowacce kungiya za’a buga ba.