Tsohuwar ‘yar takarar Gwamnan Jihar Taraba, kuma Ministar Mata a Gwamnatin Muhammadu Buhari, Hajiya Aisha Jummai Alhassan ta ce a shirya take ta marawa tsohon mataimakin Shugaban Kasa, Alhaji Atiku Abubakar baya matukar ya tsaya takara a zaben 2019.
Ta ce sam ba ta tsoron ajiye aikinta na yanzu matukar bukatar hakan ta taso, domin ta dogara da Allah wanda yake bada mulki a lokacin da ya so.
A hirarta da sashen Hausa na BBC, Hajiya Aisha ta ce ‘yan adawa ne ke yi wa furucinta mummunar fahimta. A cewarta, da ma can ita tana goyon bayan muradun Atiku Abubakar, kasancewarsa ubangidanta, saboda haka ba ta ga dalilin da za ta juya masa baya ba.
Ta ce, koda Buhari zai tsaya takara a 2019, duk da cewa har yanzu bai nuna sha’awarsa ba, kuma shi ma Atikun bai ce mata zai tsaya ba, amma matukar su biyun za su tsaya, to za ta goyi bayan Atiku.
‘’Ina girmama Muhammadu Buhari a matsayinsa na Shugaban Kasa, kuma zan ci gaba da girmama shi a har karshen rayuwata, kasancewar mutumin kirki ne da ya san ya kamata.’’