Connect with us

Uncategorized

Ba Neman Shugabanci Ne Ya Dawo Da Mu APC Ba, Cewar Yarima, Hadimin Shekarau

Published

on

ALHAJI YAKUBU YARIMA fitacce ne kuma jigo a tafiyar siyasar gidan Sardaunan Kano, Malam Ibrahim Shekarau. Haka nan kuma shi ne mai bai wa tsohon gwamna na Kano shawara kan harkokin siyasa. A wannan tattaunawar da ya yi da wakiliyar LEADERSHIP A YAU LAHADI, BILKISU YUSUF ALI, Yarima ya yi bayani kan badakalar siyasar da ke faruwa a jihar ta Kano, wacce ta kai ga sauya shekar mai gidan nasa daga PDP zuwa tsohuwar jam’iyyarsu ta asali APC. Ga yadda tattaunawar ta kasance:
Alhaji Yakubu Yarima a yau an ga gabadayan Jam’iyyar APC a gidan sardaunan Kano malam Ibrahim Shekarau tun daga shuwagabannin jam’iyyar na kasa gaba ki dayansu da gwamnan jihar Kano da sanatoci da ‘yan majalisun tarayya da na jiha me ya kawo su?
A matsayin malam Ibrahim Shekarau na gogaggen dan siyasa wanda ya yi gwamna har karo biyu ya yi ministan ilimi a tarayyar Najeriya ba abin mamaki ba ne duk irin mutumin da ki ka gani don shi ma yanzu jigo ne a kasar don duk wadannan mutanen sun zo gun malam ba a bin mamaki ba ne. Sannan halin da muka samu kanmu a cikin jam’iyyar PDP shi ma a bayyane ya ke.
Maganar da ake ta yi kasa-kasa kenan ta ana zawarcinku wadda aka ce kun musanta wato ta komawarku APC za ta tabbata kenan?
Wannan haka yake mun fice daga cikin jamiyyar PDP gobe in Allah ya kai mu Asabar maigirma Sardaunan Kano malam Ibrahim Shekarau zai sanar a hukumance cewa mun shiga APC da yardar Allah kuma ma ga yadda jam’iyyar PDP za ta ci gwamnatin jihar Kano.
Amma me ya yi zafi haka alhali a baya kuna ta murna da zuwan baki?
jam’iyyar PDP Karkashin jagorancin wanda yake rikonta a yanzu mu muka fara cewa muna murna ga duk wanda ya shigo jam’iyyar PDP kamar inda mu ma muka shiga amma Injiniya Rabi’u Musa Kwankwaso ya dawo jam’iyyar PDP. Shugabancin jam’iyyar PDP na kasa baki daya ba tare da ya tuntubi jagoranmu Malam Ibrahim Shekarau ko Ambasada Aminu Bashir Wali da Distinguish senator Bello Hayatu ba kawai sai muka wayi gari an ce an rushe shugabancin jam’iyyar PDP na jihar Kano. Wadanda aka ruguza din nan su ne wadanda aka kira su da ‘yan boko haram, su ne aka kira su da masu kisa, su ne aka kira su da barayi, su ne wadanda aka kira su da berayen dinka, su ne wadanda suka yi taro aka sa tsintsiya aka share wajen saboda su din nan masiba ne kuma annoba ne, su ne wadanda suka rike jam’iyyar PDP a lokacin da ba wanda ya isa ya shiga ko’ina ya yi tallanta a Kano saboda halin da take ciki a wannan lokacin. Amma a ce wadannan shugabannin da suka raya jam’iyyar har kowa yake sonta yanzu sai uwar jam’iyyar ta kasa ta ga ai wadannan mutane ba su da amfani a ruguje gaba daya shugaancin. Wadannan da suka shigo jam’iyyar a yanzu a ba su jagorancin jam’iyyar. Wannan shi ne makasudin da ya sa muka ce a’a a yi hakuri mun yarda maigirma Injimiya Rabi’u Musa Kwanwaso mutum ne da shi ma yake da matsayi da girma a tsaya a kalli shugabancin nan in ma so ake yi sai an ruguza a yi abin da yake na adalci a ba wa malam Ibrahim Shekarau kaso 33 a ba wa kwankwaso kaso 33 sannan a ba wa dattijo Ambasada Aminu Wali kaso 34 in an hada kaso 100 ya tabbata. Sai Injiya Rabi’u Kwankwaso ya ce shi ba haka aka yi yarjejeniya da shi ba shi da shuwagabannin jam’iyya na kasa ba. don haka muka ce bara mu je mu tambaye su su shugabannin kuma muka je wajen shugabannin jam’iyyar na kasa suka ce su ba a yi haka ba amma wasu tsiraru har da shi shugaban jam’iyyar na kasa ya ce a gaskiya ne sun zauna da su maigirma gwamna kwankwaso kuma sun zartas za su ba su kaso 51 cikin dari malam Ibrahim Shekarau da da ambasada Aminu Wali su je su raba 49 aka ce ina aka taba yin haka mutumin da ya shiga yau a ce shi za a ba wa duk wannan damar?To shi ne ya janyo abin da muka yi ta kokarin a kalla a duba a yi adalci a gyara suka ce a’a su sun yi kenan.
To, amma kun yi kokari don a sulhunta maimakon ficewa daga jam’iyyar?
Ai mun yi ya ma wuce ma kokari. Malam Ibrahim Shekarau a kan wannan matsalar ya bar gidansa karfe 5 na asuba ya nufi Abuja ya bar Abuja karfe 7 na dare ya nufi Delta ya bar Abuja ya sauka lagas karfe 9 na dare ya nufi Abekuta gun neman da Obasanjo akan duk gyaran duk wata hanya akan jam’iyyar PDP ta kalli abin nan ta kawo maslaha amma suka ki yarda su sauya wannan kaso 51. Hatta caretaker kwamiti da aka kafa shugaban nin nan namu sai ji suka yi an kafa hatta ni an sa ni mataimakin shugaan riko aka kira ni aka shaida min aka yi min murna saboda daukaka ce amma da na tambaye shi da iznin malam Shekarau ne aka ba da sunana don ni ban isa in fito ko daga daki na ne ba in dai a siyasa ne ba da izinin malam ba duk daukakar da na samu duk matsayin da na samu duk arzikin da na samu duk wata ni’ima da Allah ya yi min a siyasance na sa ne ta ne albarkacin Sardaunan Kano ni kuma ban iya butulci ba tunda shi ya kafa ni don haka sai na ce a bar ni na je na nemi izni a wajensa ina zuwa wajensa ya ce wannan shiriritar ba mu yarda da ita ba . A take na ajiye mukamin. Wannan muka duba muka ga ba za a yi mana adalci ba.
Kamar lokacin da za mu bar APC ne haka aka yi ta zawarcinmu a karshe shugaban kasa ne ya zo daga PDP da kansa ya zo ya karbe mu haka yake ma a yanzu an san nauyin sardauna . Mai magana da yawun shugaban jam’iyya na kasa dan Kano ne ya san azabar da Kwankwaso ya yi masa har ya fito a guje lokacin maigirma sardauna Shehu Yusuf Kura ya taho maigirma Sardauna ya yi masa tara da goma ta arziki amma shi ya shig gidan radiyo yana fadin wa ye sardauna ko da sardauna ko ba Sardauna jam’iyyar PDP za ta ci zabe, ya tafi APC din.
To me ne makomar magoya bayanku wmusamman ‘yan takarkari da suka riga har suka sayi fom?
Kamar tafiyar farko waccan lokacin da muka koma PDP kaso saba’in cikin dari sun biyo sardauna haka yanzu ma kaso 75 cikin dari su ma sun biyo sardaunan Kanon wadanda suke takarar gwamna su 11 amma goma daga ciki sun biyo Sardauna, shuwagabannin jam’iyya tun daga kan deputy chairman shi shugaban jamiyyar dan tsohuwar ANPP ne zuwa shuwagaannin jam’iyya , hatta principle ofisa su ma mafiya yawa sun biyo sardauna. In takaita miki dukkan mataimakan shugaban jam’iyya su ma mafiya yawa biyu cikin kaso uku sun biyo malam. Hatta chairman din ciyamomi na forum 44 local gobt wanda yanzu shi ne chairman din ciyamomi na forum north west na jamiyyar PDP yanzu haka shi ne ciyaman din ciyamomi na duk jahohin Najeriya 36 har da Abuja Alhaji Kabiru Bello Dandago amma ya hakura da wannan matsayin ya biyo Sardaunan Kano yau sun yarda za a yi wannan tafiya da su.
Kwankwaso da zai koma PDP an yi da shi wasu adadi na mukamin jam’iyya da za a ba shi, to kuma an yi irin wannan yarjejejeniyar da ku da za ku koma APC?
Wallahi mu ba mu yi wani alkawari ba, mu zuwa muka yi a ci zabe mu tsira da mutuncinmu wanda haka muka so mu yi da Kwankwaso ya ki yarda. Mu ba ma bukatar mukamin jam’iyya ko da na masinja mu ba mu yi wata yarjejeniya ba ko a jaha ko a tarayya ana ta ihun a ba mu mataimakin gwamna mu ba mataimakin gwamna ne bukatarmu mu ba, tsira da mutunci ne a gabanmu ai ko lokacin da muka shiga PDP mu ba mu yi yarjejeniya da su ba amma Allah ya ba wa sardauna Minista. An yi zawarcinmu kuma mun yarda za mu shiga jam’iyyar APC ba wata yarjejeniya.
To amma ina makomar mabiya bayanku kenan?
Ai sun yarda da jagorancin sardauna kuma ba su yi wata nadama ba. Akwai wadanda duk sun sayo fom dinsu wani ya sayo na miliyan biyu da rabi a halin rayuwar nan da ake ciki suna nan jingim kuma ba za a mayar musu da kudinsu ba amma ba sa nadama sun gamsu kuma ya tara su ya fada musu bai yi yarjejeniya da Ganduje ba ko gwamnatin tarayya don haka mun shigo burinmu a ci gwamnatin jiha da tararayya.
To yanzu ga ku a jam’iyyar APC ya ku ke kallon zaman ba za ku shiga a bare ko kuna dari-dari ba?
Ai tarihi ne ya maimaita kansa in dai za a fadi jam’iyyar APC ai sai an sa da maigirma Sardauna. Malam Shekarau na jamiyyar PDP za a yi wani bikin cikar shekara na APC taron bai cika ba sai da aka gayyaci Sardaunan Kano shugaban kasa Muhammadu Buhari yana wajen sardauna shi kadai ne dan PDP da ya zo saboda baka isa ka hada tarihin APC babu Sardauna ba. Lokacin muna PDP sardauna ya kalubalance su ya ce babu wata sadara kwaya daya a consutushan din APC wand ba shi ya rubuta shi da hannunsa ba. Ba wanda zai ce mu a APC bare ne ? mu muna fada duk wanda yake APC arzikin sardauna ya ci domin sardauna da guminsa da jikinsa da rayuwarsa da dukiyarsa aka yi APC. Maigirma Sardauna danmajalisar sarki ne a yanzu ya taba ajiye rawaninsa na wata shuda don kafa jam’iyyar APC.
A wata tattaunawarmu da kai a jaridar nan na ce maka anya zama tsakanin Sardauna da Kwankwaso zai yi wu kuwa? Amma a lokacin ka nuna lafiya lau za a zauna. Ba ka hango wannan tirka-tirkar ba?
Wallahi mu da kyakkyawar niyya muka karbe shi .Ni ne mutum na farko da na mike a fadar Sardauna na yi kirari na ce Kwankwasiyya aka amsa. Wani garin ya fi gaban kunu saboda isata a wajen Sardauna lokacin da ‘yan kwankwasiyya suka kawo ziyara gidan Sardauna ni na fara cewa kwankwasiyya daga nan muka dauka muka ci gaba da fada. Mu a tunaninmu siyasa ce duk irin muzgunawar da Kwankwaso ya yi wa malam ta wuce haka shi ma Malam duk abin da ya yi wa Kwankwaso Magana ta wuce kamar yadda Sardauna ya ce mu zo mu hada kai a ci zabe a Kano amma shi Maigirma kwankwaso yana ganin ba wanda ya isa ya bi sai dai a bi shi to wannan ra’ayinsa ne wanda za su bi shi su sai su bi shi mu dai ba za mu iya bin sa ba a yanzu
To ya tafiyar take tsakanin Malm Da shugaban kasa Muhammadu Buhari?
Shi ma wannan muna kallonsa amma mu siyasa muka fito yi, a wadanda suke tutiya yau suna Buhari ne duk malam yana gabansu don ya fi su kusa da Buhari.Sabani ne na siyasa idan maigirma shugaban kasa ya ga zai iya ci gaba da tafiya da Sardauna a APC ba damuwa amma shi maigirma Sardauna ba ya shigo don mukami ba. Mu ba mu zo don rigima da Buhari ba, mun yarda Shugaban kasa ne mun yi shi a farko ni din nan na taba fita daga gidana da riga daya na je na yi kwana ishirin wanda Sardauna ya aike ni don aikin Buhari. In akwai mutum biyar da ake aika wajen General Buhari to sai an sa Yakubu Yarima don haka nasan wa ye Buhari a bay aba ma Sardauna ba mu kanmu Yaran Shekarau Buhari ya mutuntamu.
Ya ka ke ganin tafiyar Ganduje da Shekarau?
Ai akwai alaka tsakanin Malam Shekarau da Maigirma Dr Abudullahi Umar Ganduje tun kafin ma su sami mulki dukkansu sannan bayan sun sami mulkin. A bangaren iyalai kin di san zumunci irin n mata akwai fhimta kwarai tsakanin iyalansu babu wata baraka tsakani.Sannan malam ba mai kwadayi ne ba a za a taba samun matsala ba don mu ba mu shiga jamiyya da niyyar a ba mu mukami ba ko don a ruguza mulkin shuwagaannin jam’iyya a ba mu mu un zo da niyyar hidimtawa jam’iyya in zabe ya zo mu zabi duk wani da ke jam’iyyar tun daga sama har kasa. Za mu yi wa Buhari da Ganduje aiki mu zuwa muka yi a yi siyasa a yi damukuradiyya a zabi mutanen kirki.
To ya ka ke ji kuna da karfin kada PDP a Kano?
Don Allah mu fadawa kanmu gaskiya murahu uku ne a Kano akwai tsofaffin murafu biyu da sabon murhu daya.( wato gwamna mai ci yanzu Dr Abdullahi Umar Ganduje) Idan Malam suka hadu da Kwankwaso in ba karfin mulki ba ba abin da zai hana gwamnati faduwa ko zai ci sai ya sha wahala kafin ya ci zabe.Haka idan Ganduje suka hade da Kwankwaso duk wata jam’iyyar adawa sunanta fadaddiya don sai ta fadi haka idan Sardauna ya hadu da Dr Abdullahi Ganduje to ko na rantse ba zan yi kaffara ba sai jamiyyar PDP ta fadi a Kano an gama.Don ban ga ta inda za ta yi mulki a Kano ba. Yau Allah ya hada Sardaunan Kano da Dr Abudullahi Ganduje don haka PDP ba su isa su ci komai a Kano ba a zaben da za a yi.
Wasu na ganin Sanyin Malam Ibrahim Shekarau ne ya yi yawa ba ya iya shi ma hayaniyar da rigima don ya kwaci hakkinsa bai iya jajircewa sai dai ya bar jam’iyya in ya ga za a usguna masa da magoya baya?
Ai hakuri ado ne ba kowa Allah ke ba wa ba. Mun yarda ba kowa Allah ke ba wa hakuri ba sai wanda ya zaba. Ai hakurin da Malam Shekarau yake yi ba ya zame masa illa ba , mu ba ma so ya zama dan ta’addar . ya ci gaba da sanyinsa in ya shiga wancan ramin an takura masa ya fito ya koma wani ramin. Da muka fita daga APC muka koma PDP ba mu kunyata ba , ba mu kaskanta ba haka yanzu da muka dawo APC muna yi wa Allah kyakkyawan zato ba wata wahala a tare da mu za mu ji dadin da ba mu sha ba a baya
Mene ne fatanka?
Fatanmu mu sami hadin kai a wannan haduwa da muka yi da ‘yan’uwanmu na APC tunda a mu shigo za a sami gutsattsarin magana duk da mu magana ba ta damunmu illa mu muna son a sami fahimta kowa ya ji a ransa ba mu shigo don tozarta wani ba, mu aka yi wa mu ka baro zalunci ne aka yi mana muka baro ya za mu so a yi wa wani? Mu mu zo don a sami nasara. Kuma Alhamdulillahi mun zo a dai-dai gabar da zabe ne za mu tunkara za mu fita a yi yakin neman zabe da mu a ci nasarar yakin in Sha Allah.
Haka duk wani da ke PDP manya da kanana mu na yi mu su fatan alheri muna mutunta su muna girmama su. Za mu yi zaman arziki da mutunci kaddara ce ta kawo rabuwarmu a mu’amala ba mu rabu muna nan tare a siyasa ne kadai muka rabu. Akwai wadanda har abada ba za mu iya rabuwa da su ba don sun karrama mu sun mayar da mu ‘ya’ya. Ko shi ma wannan shugaban Jam’iyyar PDP Sakandas mun ji wai ashe ramuwa ce ya yi wai sardauna bai goyi bayansa ba wannan shi ya sa ya ke bi ta da kulli to ko zaman ma mu ka yi zaman ba zai yi ma na alheri ba don ya na rike da mu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: