Ba Ni Da Burin Da Ya Wuce Isar Da Sako A Cikin Harkar Fim -Fati Gwammaja, Matar Sambo

Fim

Daga Mukhtar Yakubu,

Fitacciyar Jaruma Fatima Muhammad Gwammaja wadda aka fi sani Aminar Sambo a cikin shirin Kwana Casa’in, ta bayyana harkar fim a matsayin wata sana’ar da ta ke alfahari da ita musamman a wannan lokacin da duniya ta san ta bayan shafe tsawon shekaru da ta yi tana harkar fim, amma sai a yanzu ne Allah daukaka ta bayan da ta samu shiga cikin shirin Kwana Casa’in na Arewa 24, wanda a yanzu duk wanda ya ke kallon shirin to ya san Amina Matar Sambo, saboda irin zaman da su ke yi, musamman wajen kula da ‘yar su, kasancewar kowa da in da ya sa gaba, wajen ganin yadda rayuwar ‘ yar ta su za ta kasance.

A cikin tattaunawar su da Jaridar Leadership A Yau Asabar, jarumar ta bada mana tsawon zaman ta Masana’antar finafinai ta Kannywood, da kuma yadda ta samu kan ta a cikin shirin Kwana Casa’in, don haka sai ku biyo mu ku ji yadda tattaunawar ta kasance.

Da Farko Za Mu So Ki Gabatar Da Kan Ki Ga Masu Karantun Mu

To Assalamu alaikum, ni dai suna na Fatima Muhammad Gwammaja, wadda aka fi sani da Amina Matar Sambo, a cikin shirin Kwana Casa’in na Arewa 24. Kuma ni ‘yar Kano ce an haife ni a Karamar Hukumar Dala a unguwar Gwammaja. Kuma na yi karatu na na firamare Sakandare har zuwa N C E kuma iya nan na tsaya ban ci gaba ba a bangaren karatu.

Za ki kai kamar shekara nawa da shigowa cikin harkar fim?

To gaskiya zan kai shekaru 8 zuwa 9 a cikin masana’antar akwai lokacin da na dan samu wani lokaci ba na cikin harkar sai yanzu na dawo aka ci gaba da yin harkar da ni, amma idan zan yi bayani, zan yi ne tun daga lokacin da na shigo zuwa yanzu. Amma dai a rayuwa ta ba tashi ne da soyayyar fim, saboda kusancin da na ke da shi da kamfanin Sarauniya da ya ke a kusa da gidan mu ya ke, amma dai lokacin da kamfanin ya yi tashe muna aji daya a firamare, don haka a wannan lokacin ba mu Isa ba ma a saka mu a fim ko da mun kai kan mu. Amma dai ina bibiyar wadanda su ke yin fim din a Sarauniya, don na ga an saka ni, kowa sai ya ce sai na girma. To har dai Sarauniya suka daina fim Allah bai sa sun saka ni a fim din su ba, kuma ko da na ce zan shiga ma iyayena ba za su so ba. To daga baya ne da na girma na shigo masana’antar, lokacin da ta dawo Zoo Road kuma a nan na samu damar da aka fara saka ni a fim.

Ya aka yi kika samu kan ki a fim din kwana Chasa’in?

To kamar yadda aka saba al’adar fim din Arewa 24 ana kiran taron tantance jarumai ne domin a samu wadanda suka dace da aikin, to nima haka aka yi lokacin da aka kira za a tantance jaruman sai na je na yi kuma Allah ya ba ni nasara a kan matar Dan daban fim din wato Sambo, wadda na ke da ‘ya Ummi a cikin shirin, kuma gaskiya na ji dadi sosai don lokacin da aka kira ni ban dauka babban fim ba ne, kuma ban taba zuwa an tantance ni ba in za a saka ni a fim haka a ke saka ni kamar yadda aka saba yi a masana’antar mu, kuma lokacin da na je zan yi na tarar da mata sama da guda dari, a kan wannan rol din kuma sai Allah ya sa ni zan hau rol din.

Ya kika samu kan a cikin shirin Kwana Casa’in?

To kamar yadda masu kallo suka gani, na taka rawa ta matar aure, wacce take da ‘ya, kuma shi rol din da na taka kullum ina kokarin na ga na ba’ ya ta tarbiyya, to Amma duk da kokarin da na ke yi a kan hakan, shi kuma miji na yana kokarin bata mini, domin ya dauki son duniya ya dora mata, ba shi da wani buri da ya wuce ‘yar, bai damu da karatun ta ba, kawai dai ya fi damuwa da Nishadin ta, to gaskiya na yi ta kokarin ganin ‘yar ta samu cikakkiyar kulawa da tarbiyya, amma dai hakan bai yiwu ba. To gaskiya wannan rol din da na yi ya ya ba ni wani karsashi har ina jin kamar ni matar aure ce da na ke kula da rayuwar ‘ ya ta don haka na ke ganin kamar mijina ne da  ‘ya ta a gaske. Kuma hakan ya sa Kara fatan nan gaba na samu kaina a gidan miji ina zaune da yara na a matsayin Uwa.

Wanne irin buri kike da shi a cikin harkar fim?

To buri na dai shi ne kullum na ga ina isar da sako, ta kowanne bangaren, ko ta aktin ko ta murya domin ina wasan kwaikwayo na rediyo kuma shi ma harkar isar da sako ne gaskiya ni ba ni da burin da ya wuce na ga ina isar da sako a cikin harkar fim.

Fati kin taba yin aure ko Sai nan gaba?

To ka ba ni dariya da ka tambaye ni a kan ko na taba aure. Ka san dai ni cikakkiyar kabilar Hausa ce iyayena ba za su zauna da ni ba tare da sun yi mini aure ba, to nima iyayena sun yi mini sutura da dakin miji sun aurar da ni, zama ne dai bai yi dadi ba muka rabu da miji na, kuma bayan auren ya mutu ne na sake dawowa cikin harkar fim. Muna fatan dai Allah ya kawo wanda zai rike ni na zauna a gidan aure Lafiya.

Idan na fahimta dai yanzu Fati a kasuwa take.

Fadi ka kara ni yanzu a kasuwa nake, ina fatan Allah ya kawo miji nagari.

Wacce shawara za ki bai wa abokan sana’ar ki?

To shawarar da zan ba su kuma har da ni ma, jarumai su sani duk lokacin da mutum ya fitar da fuskar sa duniya ta san shi, to hankalin mutane yana dawowa kan sa ne, don haka sai mu rinka taka tsan tsan da rayuwar mu, domin wani zai zo ya nuna yana son mu, amma da wata manufa ya ke yi ba don Allah ba. Don haka sai mu rinka kiyayewa, musamman a game da Bideo Call, domin yana daya daga cikin abin da ya ke sa wa mu samu Matsaloli, kina gida a kwance, sai a kira ki Bideo Call ki daga ba tare da kin kula da yanayin da kike ciki ba, kuma wannan ya kan sa idan abin ya fita a samu matsala don haka jarumai a rinka yin taka-tsan tsan, don gudun abubuwan da za su zame mana matsala.

To madalla mun gode.

Nima nagode.

 

Exit mobile version