Ba Ni Da Hannu A Daukar Nauyin IPOB –Jonathan

Daga Muhammad A. Abubakar

Tsohon Shugaban Najeriya, Goodluck Jonathan, ya ce ikirarin da Ministan yada labaran kasar, Lai Mohammed, ya yi na cewa wai ‘yan hamayya ne ke daukar nauyi tare da ingizo ‘yan kungiyar masu fafatukar kafa kasar biyafara.

Jonathan ya nuna cewa har yanzu gwamnatin Buhari na ci gaba da yada farfaganda maimakon mayar da hankali kan aikin da al’umma suka zabe ta domin shi.

A wata sanarwar da Reno Omokri, mataimaki na musamman kan shafukan sadarwar zamani ga Shugaba Goodluck Jonathan, ya wallafa a shafin kafar ‘Facebook’ na tsohon shugaban kasar, cewa idan gwamnatin Nijeriya ta san ‘yan hamayyar da ke daukar nauyin ‘yan IPOB, ta kama su tare da gurfanar da su gaban kotu, ba wai ta tsaya cika baki ba.

Mista Jonathan ya ce bai dace a yi amfani da sojoji wajen dakile laifuka a cikin gida ba, domin an ba su horarwar yakar abokan gaban kasa da ke waje ne.

Ya ce maimakon sojojii, ‘yan sanda ne ya kamata a yi amfani da su wajen kwantar da tarzomar cikin kasa.

Tsohon shugaban Nijeriyar ya kara da cewar, idan sojoji suka fara yi wa fararen hula barazana, to maimakon a kwantar da tarzoma sai hakan ya zama barazana ga mutane.

 

Exit mobile version