Tsohon shugaban riko na jam’iyar PDP ta kasa, Sanata Ahmed Mohammed Makarfi ya karyata bayanan da suke cewa yana da muradin tsayawa takarar Sanata a zaben 2019 da ke tafe.
Makarfi wanda ya nemi tikitin tsayawa takarar shugaban kasa a karkashin PDP da shi da wasu mutum 11 ya fadi ne a ya yin da mataimakin shugaban kasa Alhaji Atiku Abubakar ya yi galba a kan dukkaninsu da kuri’u masu tulin yawa.
Rahotonin sun yi yawo kan cewar shi dai Makarfin yana shirye-shiryen fitowa neman kujerar Sanata a babban zaben 2019.
Tsohon gwamna, ya shaida ha kan ne a ta cikin wata kwafin sanarwar da ya aike wa manema labaru dauke da sanya hanun Kakakinsa, Mukhtar Sirajo ya shaida cewar shi dai bai da wani muradi makamancin wannan, ya shaida cewar zancen babu gaskiya ko kadan a cikinsa.
Ya ce a maimakon haka, dukkanin ‘yan takarar da suka samu nasara a jam’iyyar wadanda aka zabesu a ya yin fidda gwani suna da cikakken iko da damar da zasu yi daukaka darajar tutar jam’iyar a idon duniya har ma ta kai ga nasara, don haka ne ya nemi su yi ha kan.
Ya ce, ya yi amanar cewar sauran jama’a kuma kamatuwa ya yi su karfafe su da mara musu baya wajen ci gabantar da harkar demokradiyya.
Ya dai shaida cewar shi dai babu wani yunkurin da yake yi na tsayawa takarar sanata a zaben 2019 don haka ne ya nemi masu hada wancan labarin da masu jinsu da su daina domin bashi da muradin ha kan.