Ba Ni Na Dau Nauyin Taron Masarautar Ilorin Ba —Lai Mohammed

Makaman

Ministan yada labarai da al’adu, Alhaji Lai Mohammed, ya musanta zargin da ake ma shi na daukar nauyin watsa bukin ranar Kirsimati wanda aka lalata shi wanda ‘yan asalin Masarautar Ilorin suka shirya.

Taron na shekarar 2018, na ‘yan asalin Masarautar ta Ilorin, an yi shi ne a haraban fadar Sarkin na Ilorin, wanda wasu zauna gari banza da ake kyautata zaton ‘ya’yan Jam’iyyar APC da na Jam’iyyar PDP suka tarwatsa shi, inda suka yi ta iface-ifacen taken Jam’iyyun su a lokacin da ake gabatar da kalandar kungiyar.

Da yake amsa tambaya daga manema labarai a Ilorin, ranar Juma’a, Ministan ya karyata zargin da ake yi ma shi, na cewa da gangan ya dauki nauyin shirya yayata taron kai tsaye a tashar talbijin ta kasa domin ya baiwa Sarkin na Ilori, kunya.

Ministan ya nisanta kansa daga zargin, yana mai cewa, sam bai ma san za a yi taron ba.

Ya zargi Jam’iyyar PDP a Jihar ta Kwara da yada wannan jita-jitar, ya yi nuni da cewa, Jam’iyyar tana ta faman yada labaran karya a kansa a ‘yan kwanakin nan domin ta ga ta hada shi fada da Masarautar ta Ilorin.

Ya bayyana cewa, a yanzun haka an gurfanar da mutane 10 a gaban kotu masu alaka da yamutsin da aka yi a fadar ta Ilorin, da kuma wasu batagari da suke da hannu a lalata alamomin Jam’iyyar ta APC a Ilori.

Ministan ya ce, mutane a Jihar ta Kwara, sun gaji, a shirye kuma suke da su samar da canji a wajen shugabancin Jihar, don haka ba wata tursasawa ta bata suna da ta isa ta hana a kawar da Jam’iyyar ta PDP daga shugabancin Jihar a babban zabe mai zuwa.

Exit mobile version