Ba Ronaldo Ne Kawai Zuciyar Real Madrid Ba -POCHETTINO

Mai koyar da ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Tottenham, Mauricio Pochettino ya bayyana cewa akwai yan wasan ƙungiyar dayawa waɗanda suke taimakawa ƙungiyar sosai ba kawai Ronaldo bane.

Pochettino ya bayyana hakane a gaban yan jaridu a shirye-shiryen da ƙungiyarsa takeyi na fafatawa da real Madrid a wasan zakarun turai a ranar talata a filin wasa na Barnabue dake birnin Madrid.

Yaci gaba da cewa, Ronaldo ɗan wasa ne ƙwararre, kuma yanada zuciya inda ya cehakan ne yasa ɗan wasan ya lashe kyautar gwarzon ɗan ƙwallon duniya har sau hudu kuma yana saran wannan shekarar ma shine zai lashe.

Ya ƙara da cewa real Madrid sunada manyan yan wasa da babban mai koyarwa, kuma kowanne bangare yana taimakon ɗan uwansa a ƙungiyar don ganin ansamu nasarar da ake buƙata.

Yace, Ronaldo kamar Messi ne a Barcelona, babu kamarsu a ƙungiyoyinsu amma duk da haka suna buƙatar taimakon abokan wasansu domin samun nasarori.

Ronaldo dai yazura ƙwallo a raga a wasan da suka fafata da ƙungiyar Getafe a wasan laliga a ranar asabar din data gabata kuma itace ƙwallo ta farko da ya ci a wannan kakar kuma a ƙwallo ta shida a wannan kakar a dukkanin wasannin daya buga.

Exit mobile version