Khalid Idris Doya">
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RIGAR 'YANCI

Ba Shaye-shaye Kawai Sojoji Suka Iya A Bariki Ba, Akwai Mahaddata Alkur’ani – Kyaftin Babangida

by Khalid Idris Doya
February 16, 2021
in RIGAR 'YANCI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Babban Limamin Barikin Sojoji ta Shadawanka da ke cikin garin Bauchi, Kyaftin Muhammad Yusuf Babangida ya labarta cewa a cikin barikokin soja a yanzu haka ana samun daruruwan Mahaddata Alkur’ani mai girma ba kamar yadda jama’a suke dauka duk sojan da ke cikin Bariki mashayin giya ko kayan maye ba nee.

Imam Babangida ya shaida hakan ne sa’ilin wata ziyarar kyautata alakar aiki a bangaren aikin Hajji da ya jagoranci tawagar sojoji zuwa ga babban sakataren hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Bauchi, Kyaftin ya nuna cewa sun kawo ziyarar ce domin duba hanyoyin da za su bada tasu gudunmawar wajen kyautatawa da saukaka aikin Hajji a kowace shekara.

samndaads

Ya ce: “Mutane da yawa sun dauka duk Sojan da yake zuwa Bariki to mashayin Giya ne, saboda da abun da ya faru da sojojin da suka yi yakin Biafra shi wannan yakin Basasa din an dibi mutane ne kawai ba a kan akida ba, amma daga baya al’amarin ya canza.

“To ka ga a yanzu idan ka je Bariki dole za ka tabbatar akwai musulmai, ni da na zo nan zuwa yanzu ina da shekara uku don na zo a 2018 dalibai da na tarar ba su wuce mutum 200 ba, amma yanzu haka ina da dalibai na Islamiyya da Hadda sama da 560, sannan zuwa yanzu na samu sauka kusan sau uku, muna gayyatar mutane daga cikin gari domin su halarci bikin yaye dalibanmu da suka Haddace Alkur’ani.

Ya ce, a bisa dabarun da ya fito da su domin kyautata Haddar yaran sojoji da kuma ba su damar gogewa a fagen karatun Kur’ani daidai da sauran makarantun Islamiyoyi ya kai shigar da daliban makarantarsu gasa da neman sa’a a tsakanin sauran makarantun Hadda da suke jihar “A wannan makarantar ta mu da muke yi, sai na ga in mu-ya-mu ne a Bariki ba za a san abun da muke yi ba; sai na nemi wasu makarantu a cikin garin nan na Bauchi da duk shekara sukan yi Musabakar Karatun Alkur’ani na yi rijista da su duk shekara mukan dibo daliban makarantarmu su zo. Duk da cewa bara ne muka fara a bana ma yaranmu za su shiga kuma za mu tabbatar duk shekara yaran sojoji na shiga ana damawa da su a fagen karatun Kur’ani a jihar nan.

“Muna da daliban da suke da Haddar izu 30 akwai masu 20 zuwa kasa akwai kuma wadanda sun zarce hakan. Dukka daga cikin ‘ya’yan sojoji wasu ma iyayensu sun mutu a Maiduguri amma mun tsaya a kan su har sai sun samu Haddar Alkur’ani.”

Ya yaba tare da nuna gamsuwa da salon jagorancin da babban sakataren hukumar ke yi, sojan ya nuna cewa akwai gayar alfanu wajen ilmantar da maniyyata yadda za su gudanar da aikin Hajji domin basu damar yin ayyukan kamar yadda addini ya shimfida domin samun damar yin Hajji karbabbiya, a bisa hakan ne ma ya jinjina wa kokarin babban sakataren hukumar na bada himma a fagen ilmantar da maniyyata a kowani lokaci.

Tawakar sojojin sun baiwa hukumar kula da jin dadin alhazai ta jihar tabbacin samun kyakkyawar hadin kai da goyon baya a yayin aikin hajji a kowace shekara tare da tabbacin bada tsaro mai nagarta.

Da ya ke maida martani kan ziyarar, babban sakataren hukumar kula da jin dadin Alhazai ta jihar Bauchi Alhaji Abubakar Babangida Tafiya ya nuna matuwar farin cikinsa da ziyarar tare da nuna hakan a matsayin Matakin da zai kara masa kumaji da hiar bada kokarin wajen kyautata aikin Hajji.

Ya nuna sojoji a matsayin abokan jere a fagen aikin Hajji, sai ya nemi cewa za su ci-gaba da yin aikin hadaka domin kyautata aikin Hajji a kowani shekara. Ya gode wa rundunar soja a bisa bada tasu gudunmawar wajen kyautatawa aikin Hajji.

Tafidan Giade, ya ce hukumomin tsaron sun taimakawa sosai ta fuskacin kula da lafiya, dukiya da rayukan maniyyata gabanin, lokacin da bayan aikin hajjin.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnonin Arewa Sun Zama Cima-Zaune – Kwamared Hauwa Kabir

Next Post

Mutanen Neja Sun Yi Murna Da Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Matan Karkara 

RelatedPosts

Su Sanata Gaya Sun Halarci Sadakar Kwana 40 Na Surukarsa A Ankpa

Su Sanata Gaya Sun Halarci Sadakar Kwana 40 Na Surukarsa A Ankpa

by Khalid Idris Doya
2 days ago
0

Daga Ahmed Muh'd Danasabe, Lokoja Ranar Lahadi da ta gabata...

Yadda Zulum Ya Ziyarci Wadanda Harin Boko Haram Ya Rutsa Da Su A Maiduguri 

Yadda Zulum Ya Ziyarci Wadanda Harin Boko Haram Ya Rutsa Da Su A Maiduguri 

by Khalid Idris Doya
2 days ago
0

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri Biyo bayan harin da mayakan Boko...

Dalilanmu Na Shirya Aurar Da Zawarawa A Kaduna – Sardaunan Badarawa

Dalilanmu Na Shirya Aurar Da Zawarawa A Kaduna – Sardaunan Badarawa

by Khalid Idris Doya
2 days ago
0

Daga Musa Muhammad, Abuja An kammala dukkan shirye-shirye don fara...

Next Post
Mutanen Neja

Mutanen Neja Sun Yi Murna Da Tallafin Gwamnatin Tarayya Ga Matan Karkara 

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version