Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
No Result
View All Result
Leadership Hausa Newspapers
No Result
View All Result
Home RAHOTANNI

Ba Ta’addanci Ba, Har Da Talauci Ya Kamata Gwamnati Ta Yaka -Shettima Kukawa

by Tayo Adelaja
September 19, 2017
in RAHOTANNI
3 min read
WhatsAppShare on FacebookShare on TwitterShare on Telegram

Daga Muhammad Maitela, Maiduguri

An yi kira ga gwamnatoci da cewa su hada yaki da ayyukan tarzoma (ta’addanci) da yaki da fatara da zaman kashe wando a matsayin dan Juma da dan Jumai; muddin gwamnatin tarayya dana jihohi da gaske suke yi; idan ka yaki ta’addanci baka yaki fatara ba, to baka yi komai ba. Saboda kamar yadda karin-maganar Turawan yamma ke cewa koyaushe ‘ the hungary-man is the angry-man’.

samndaads

Wadannan shawar-warin sun fito ne daga bakin kusa a tsohuwar jam’iyyar CPC kuma jigo a APC; babban sakataren kungiyar Buhari Support Organization, a jihar Borno, Alhaji Muhammed Shettima Kuburi, Kukawa a cikin tattaunawar da yayi da wakilin mu a jihar, a ranar litinin din wannan makon a birnin Maiduguri.

Alhaji Muhammed Shettima ya fara da bayyana halin da al’ummar jihar Borno ke ciki ta dalilin ibtila’in rikicin Boko Haram wanda ya dade yana addabar yankin. Yayin da ya ce duk da yadda zancen da ake ciki yanzu matsalar ta lafa, amma kuncin rayuwar da al’amarin ya haifar har yanzu bai bar jama’ar jihar ba. Ya ce matsalar tsaron ta shafi kowa da komai a jihar Borno; domin idan bata shafe ka kai tsaye ba, to madawakin-gobara ya same ka.

Bugu da kari kuma ya bayyana cewa” yanzu idan an ce gari ya waye, ko’ina idan ka duba kananan yara ne da mata ke watan-garereniya a kan tituna suna bara da neman taimakon abinda zasu ci; wani zubin a haka suke wuni dakyar da jibin goshi zasu samu abinda zasu ci. Sannan dole su fito bara saboda an kashe mazan su da iyayen su, yanzu basu da kowa sai wanda ya Allah ya ga Ma’aiki ya tallafa musu da sadaka”.

Alhaji Muhammed Shettima ya shaidar da cewa, bisa ga wannan yanayin suke ba gwamnatin tarayya da ta sauran jihohi kan cewa suyi amfani da dutsi daya su jefi tsuntsu biyu a cikin kokarin da suke yi na yakar ayyukan ta’addanci a Nijeriya “saboda ai Bature yana fada a cikin wani karin-maganar sa’ the hungary-man is the angry-man’. Saboda haka muna ba gwamnatoci shawara kan su hada yaki da ayyukan tarzoma da yaki da fatara da zaman kashe wando wuri guda; don mun fahimci tare suke tafiya”.

“ idan ka lura fa wadannan dubun-dubatar yara da mata da suka rasa mazajen su ta dalilin rikicin Boko Haram suna da bukatar abinci, karatu da sauran su, a lokaci guda kuma sun rasa wadanda zasu tallafi rayuwar su. To, abinda muke jin tsoro shi ne makomar su nan gaba sannan da fargabar kada su fada hannun miyagun mutane wajen amfani da su a hanyar da bata dace ba”. Ya bada shawara.

A hannu guda kuma, Shettima Kuburi ya ankarar da gwamnatoci kan cewa, suyi kokari wajen samarwa matasa ayyukan yi wanda hakan zai rage fatara zaman kashe wando, da shiri na musamman ga al’amarin yara da matan da suka rasa mazaje da iyayen su ta dalilin wannan rikicin, a lalabo hanyoyin da za a karfafa yan kasuwar da wannan hargitsin ya jawo rasa dukiyar su domin sake farfado da yanayin tattalin arzikin jihar Borno.

A gefe guda kuma Alhaji Muhammed Shettima ya yaba da namijin kokarin gwamnatin jihar Borno dangane da kokarin sake gina wasu yankunan da mayakan na Boko Haram suka rusa a jihar, sake gina makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya. Inda ya ce”gaskiya mun yaba matuka da kokarin Gwamna Hon Kashem Shettima ta yadda yake kokarin sake gina makarantu da cibiyoyin kiwon lafiya wadanda wannan rikici na Boko Haram ya shafa, gaskiya ana kokari a kan wannan kuma jama’a suna jin dadin hakan”. Ya tabbatar.

“Sai dai wani hanzari ba gudu ba, muna ba gwamnatin Borno shawara ta sake duba yanayin malaman makarantu, musamman na firamare, karfafi gwiwar su da abinda zai kara musu himma a cikin kokarin da suke yi. Har wala Ya’u, akwai bukatar gwamnatin jihar Borno da tayi wa sha’anin ilimin jihar garambawul da kwaskwarima saboda idan ka lura mafi yawan al’ummar jihar a cure suke waje guda; ba kamar da ba”.Ya nanata.

 

SendShareTweetShare
Previous Post

Gwamnatin Bauchi Za Ta Taimakawa Masu Laruran Ido Kyauta

Next Post

Jajircewar ’Yan Sanda Ne Ta Takaita Ta’addanci A Gombe -Tsohon Kwamishinan ’Yan Sanda

RelatedPosts

Alaba

‘Yan Kasuwan Arewa A Legas Mu Hada Kai Don Cigaba – Muhammadu Alaba

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Yusuf Abdullahi Yakasai, Hadin kai shi wani babban al’amari...

Jama'a

Taimaka Wa Jama’a Shi Ne Shugabanci Nagari -Matawalle Alagwadun Legas  

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Yusuf Abdullahi Yakasai,   Matawallen Alagbado, Alhaji Muhammadu ya...

Samarun

Yadda Rasuwar Matashi Ta Jefa Mutane Cikin Alhini A Samarun Zariya

by Muhammad
2 days ago
0

Daga Idris Umar, A ranar laraba ta wannan makon da...

Next Post

Jajircewar ’Yan Sanda Ne Ta Takaita Ta’addanci A Gombe -Tsohon Kwamishinan ’Yan Sanda

Leave a Reply Cancel reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *

Domin sanya talla ko karin bayani a tuntube wannan numbar +2348126152609.

Leadership Epaper
ADVERTISEMENT
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU
Advertise with us

© 2020 Leadership Group .

No Result
View All Result
  • LABARAI
  • WASANNI
  • RAHOTANNI
  • SIYASA
  • KASUWANCI
  • ADABI
  • RA’AYINMU
  • TATTAUNAWA
  • BIDIYO
  • MAKALAR YAU

© 2020 Leadership Group .

Go to mobile version