Ba Tabbas Kan Zuwan Nijeriya Gasar Cin Kofin Duniya – Garba Lawal

Lawal

Tsohon dan wasan Super Eagles, Garba Lawal ya ce, a yanzu damuwarsa ba
ta ta’allaka ba kan wanda zai zama sabon kocin Nijeriya, sai dai ta yaya ne kasar za ta samu gurbin halartar gasar cin kofin duniya a Katar. Wannan na zuwa ne a daidai lokacin da aka zafafa kiraye-kirayen hukumar kwallon kafar kasar ta NFF da ta gaggauta sallamar kocin super Eagles Gernot Rohr, wanda ake ganin ya kasa tabuka abin kirki.

Ko da yake wasu majiyoyin bayan fage masu tushe daga hukumar ta NFF sun ce, nan kusa za a kori kocin mai ruwa biyu, wato daga Faransa da Jamus, amma a halin yanzu ana kan tattara takardun sallamar sa a cewar rahotanni na bayan fagen.

Tuni wasu daga cikin ‘yan Nijeriya suka fara ba da shawarar daukar Emmanuel Amunike tare da  Salisu Yusuf  domin jagorantar tawagar ta Super Eagles, amma a cewarsa, ko da Nijeriya ta dauko Jose Mourinho a yanzu, amma ta rasa damar samun tikitin, hakan shirme ne. A cewar Garba Lawan, zancen nada koci ba shi ba ne ya dame shi, abin da ya dame shi shi ne, ta yaya Najeriyar za ta samu tikitin zuwa Katar.

Exit mobile version