Ba Tallafin Abinci Mu Ke Bukata Ba, Tsaro – Al’ummar Madagali

Daga Muhammad Shafi’u Saleh, Yola

 Jama’ar garin Madagali a jihar Adamawa, sun bayyana samar musu da tsaro da cewa ita ce babban bukatarsu ga gwamnatin tarayya, amma batun abinci ba.

Mutanen garin sun bayyana haka a lokacin da hukumar bada agajin gaggawa ta kasa (NEMA), ta kai musu tallafin kayan abinci manyan motocin tirela uku domin raba wa jama’ar yankin da ke fama da matsalar kai hare-haren Boko Haram.

Da yake jawabi a taron shugaban karamar hukumar Madagali Alhaji Yusuf Muhammad, ya ce sun ka sa fahimtar dalilin watsin da gwamnatin tarayyar ta yi da su, ya ce idan ba’a sonsu a kasar a sanar da su, su koma Kamaru.

“An yi watsi da mu ba mu san dalili ba, Boko Haram na ta kashemu, alhali bai wuce kilomita uku tsakanin gari da inda suke ba, ko mu ba ba ‘yan Nijeriya bane? Idan ba’a sonmu a sanar da mu za mu koma Kamaru mu da sarakunanmu da ‘yan majalisar wakilanmu da dan majalisar jiha da sanatarmu za mu hadu gobe mu samu gwamna ya kaimu wajan shugaban kasa, mu ji matsayin mu ko mu ba ‘yan Nijeriya bane da’ake kashe mu” inji Yusuf.

Shugaban karamar hukumar wanda ya yaba wa hukumar bada agajin gaggawa ta kasa NEMA bisa kawo masu tallafin da ta yi, ya ce “Mun gode da tallafin kayan abinci, saboda mutanen mu suna cikin yunwa, amma mu ba ragwaye bane.

Mu manema ne mu ‘yan kasuwa ne, muna neman a samar wa jama’armu tsaro, saboda su gudanar da kasuwanci da noma, za mu noma abincin da zamuci”inji Yusuf.

Shi ma a nasa jawabin shugaban hukumar bada agajin gaggawa (NEMA) ta kasa, Wanda shugaban bangaren bincike na hukumar Air Kwamanda Sunday Ohemu, ya wakilta ya ce hukumar ta damu da halin da jama’ar yankin ke ciki.

Ya ce ya ji daukacin koke-koken da mutanen garin suka yi kuma zai kai koke-koken na su inda ya dace “Na zo ne Amadadin shugaban hukumar NEMA na kasa kuma na ji koke-kokenku, zan Isar inda ya kamata” inji Ohemu.

Haka shi ma a jawabinsa Sanata mai wakiltar Adamawa ta tsakiya a majalisar Dattawa Sanata Abdul’aziz Murtala Nyako, ya ce ya ji dadi da Jama’ar suka bayyana abinda ke damunsu, ya ce ita kanta majalisar za ta duba wannan batu.

Sanata Nyako wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar kan ayyuka na musamman ya bukaci jama’ar yankin da su bada koken na su a rubuce, ya ce idan akwai wasu karin matsalolin duk su rubuta domin daukar mataki a kai.

Shi kuwa Hakimin Gulak Alhaji Bello Ijadi, ya zargi ‘yan siyasar yankin da neman wargaza garin sakamakon rashin hadinkan dake tskaninsu, ya ce idan ba su hada kansu ba, bu ranar da za su rabu da matsalar Boko Haram a yankin.

“Bai kamata sauran kananan hukumomi jama’a suna bacci yadda suke so mu mun kasa samun zaman lafiya ba, zaman lafiya ba zai samu ba sai mun hadakanmu” inji Ijadi.

Ita ma dai Sanata Binta Masi Garba, da ke wakiltar Adamawa ta Arewa a majalisar Dattawa ta nuna bacin ranta game da rashin samun gudunmawar da ta ce Jama’ar kananan hukumomin Michika da Madagali ba su cika samu ba.

Ta ce akwai bukatar gwamnatin tarayya ta bada wani hobbasa domin kyautata rayuwar jama’ar kananan hukumomin biyu dake fuskantar matsaloli da dama sakamakon ayyukan ‘yan bindigar Boko Haram a yankin.

 

Exit mobile version