Gwamnatin jihar Borno ta karyata wani rahoton da ya nuna cewa mayakan kungiyar Boko Haram sun sake kai wa tawagar Gwamnan jihar, Babagana Zulum tare da jami’an tsaron shi hari a karshen mako.
Wannan furucin ya fito daga bakin mai magana da yawun Gwamna Zulum, Malam Isa Gusau, a takardar manema labarai ranar Lahadi, inda ya bayyana cewa, Gwamnan ya tafi garin Baga a ranar Asabar domin sanya ido a aikin raba kayan tallafin abinci da kayan masarufi ga kimanin yan hijira 5,000 kana daga baya ya koma gida Maiduguri lafiya.
Isa Gusau ya kara da cewa, a lokacin da yake gudanar da ziyarar a garin Baga, domin duba muhimman ayyukan sake farfado da yanki tare da kokarin shi na ci gaba da dawo da al’ummar yankin cikin hanzari.
“Amma kuma duk wata kafar yada labaran da ke bukatar cikakken bayani dangane da irin wannan al’amarin ta na iya tuntubar rundunar sojojin Nijeriya don karin bayani.” In ji shi.
Ya ce, “Haka kuma Zulum ya yaba da kokarin sojoji, yan-sanda, da yan sinturi dangane da aiki tukuru wajen ganin jihar Borno ta samu dawamamen zaman lafiya.”
A hannu guda kuma, wasu majiyoyi a jihar sun bayyana cewa sojoji bakwai su ka mutu biyo bayan tashin wani bam din da ake zargin Boko Haram ne suka dasa shi, a lokacin da suke raka ayarin motocin kayan tallafi zuwa Baga, ranar Asabar.
Baya ga hakan kuma sai yan kungiyar su ka rinka yi wa ayarin manyan motocin dakon kayan harbin mai kan uwa da wabi, a kan hanyar su ta kai kayan abincin zuwa garin Baga na karamar hukumar Kukawa.
Haka zalika kuma, wadannan kayan abinci ne wadanda Gwamna Zulum zai jagoranci raba su ga yan gudun hijirar da aka dawo dasu garuruwan su.
Har wala yau, “An kwashe wadanda wannan harin ya rutsa dasu zuwa asibutin Maiduguri”. Ta bakin majiyar mu.
Shi ma daya daga cikin sojojin da ya tsallake rijiya da baya daga harin, ya bayyana cewa, ’yan ta’addar sun tafi da makamai da motar yaki daya.
Wani bincike ya tabbatar cewa, an kai harin ne a kauyen Gazarwa, wanda ya yi kaurin suna a matsayin tungar Boko Haram, bayan garin Gajiram, kafin shiga garin Monguno.