Ba Wanda Zai Hana Tasowar Kasar Sin, Balle Joseph Biden

Daga CRI Haus

Amurka ta san wannan ci gaba, amma gwamnatinta tana son hana bunkasuwar kasar Sin. Matakin da ba zai samu nasara ba ko kadan, ya ce Donald Trump ya gaza yin haka, balle ma gwamnatin Biden.
Yayin da ya yi tsokaci kan huldar kasashen biyu a fannin ciniki da tattalin arziki, Wolf ya nuna cewa, a cikin shekarun baya-bayan nan, bangarorin biyu sun ci gajiyar nagartacciyar huldar a wannan fannin, amma tun lokacin da Donald Trump ya hau kujerar shugaban kasar, sai gwamnatinsa ta dauki matakan da ba su dace ba kan kasar Sin.
A cewarsa, bai san dalilin da ya sa gwamnatin Trump da ta Biden suka yi watsi da dangantaka mai amfanawa juna, suka zabi hanyar yin fito-na fito da kasar Sin ba. A ganinsa, wadannan matakai tamkar fusata ne ko damuwa da tasowar kasar Sin, ganin cewa har ta kusan zarce Amurka. (Amina Xu)

Exit mobile version