Ba Wani Canji Da APC Ta Kawo A Kasar Nan Sai Kunci A Zamantakewar Al’umma -Dada

An bayyana cewa ba wani abu da mulkin jam’iyyar APC ta kawowa al’ummar kasar nan na canji illa sasu a cikin kuncin rayuwa. Shugaban jam’iyyar PDP na karamar hukumar Birnin Kano, Alhaji Sabo Ahmad Dada ya bayyana hakan a zantawarsa da manema labarai.

Ya ce kowa ya kalli yanda al’amura ke tafiya an samu koma bayane a kasar nan komai ya tabarbare mutane suna cikin kuncin rayuwa,ba ilimi,ba hanyoyi,ba wuta ba ruwa ba aikinyi komai ya koma baya babu ma alamar sunaso su gyara.

Alhaji Ahmad Sabo Dada ya ce takai yanzu al’ummar kasar nan na cewa dama za a dawo da kasar yanda PDP ta basu da ya fi saboda a wannan lokacin akwai walwala da jin dadi.

Shugaban na jam’iyyar PDP na karamar hukumar birni ya ce duk lokacinda masu mulkinnan suka gaza sa suce haka suka sami kasar,hakan sai ya bashi dariya saboda in aka yi duba da wannan wahala da yan kasa ke ciki me yasa a baya basu shiga ba? Da suke cewa PDP ta kashe kasar da suka karba sun taradda mutane a cikin kuncin rayuwane? Sai da suka karbeta cikin wata daya abu ya rikice musu kaya suka rika tashi.

Ya ce an ce, PDP ta shekara 16 tana bata kasa a cikin shekarun nan ba inda aka sai mai Naira 145, ba inda aka sayi buhun shinkafa sama da Naira 10, 000.

Wane hikima PDP ta rika yi mutane suka rika samun abubuwan masarufin rayuwa cikin sauki da kwanciyar hankali?

Dada ya kara jaddada cewa, “babu wani abu da APC zasu nuna,basuzo da basuzo da tunanin yanda za suyi mulki ba,basu taba zaton dan’Nijeriya zai zabesu ba saboda haka basuda”blueprint”saida aka karbi mulki aketa kame”kame,wannan shi ne abin da yake faruwa daga sama har kasa na mulkin APC.Saboda haka mutanen kasar nan sun zabi mutane da da ba za su iya mulki dan kyautatawa musu ba.Dan haka ya kamata nan gaba su bude ido su zabi jam’iyyarda ya kamata.

Ahmad Sabo ya ce yasan PDP itace  yan kasar nan ya kamata su zaba,dan in aka zauna aka natsu za aga mulkinda APC ta kusa shekara uku tana yi da ita ta shekara 16 da PDP ta yi ana cewa ta kashe kasa kuma har yanzu damakwaradiyya ake.anya ba kasa bane?Yan kasa su zabi mutanen kirki matasa ba wanda suka shekara 70 ko 80 ba.kazo ka zabi mutum mai zaiyi maka?

Alhaji Ahmada Sabo Dada ya ce yanzu kamar Gwamnan Kano Ganduje ne,tunda yazo bashida wata magana saita kakabawa mutane haraji ga wahala ga komai amma haraji ake nema,talakawa.ma’aikata,yan kasuwa haraji, gashi an kakabawa wa ma’aikata biyan kudin inshorar lafiya dole a zaftari kudi a dan albashinda ake basu wanda baya ma isarsu saboda halin kuncin matsi da tsadar rayuwa da APC ta jeja al’umma a kasar nan.

Ya kara da cewa ga Asibitoci ba magani,an farke tituna a kano da sunan aiki ba a yi.Ya kamata al’ummar Kano da dukkan yan kasa su gane cewa ana cewa an fta daga matsin tattalin arziki a kasar nan kamar yadda mataimakin shugaban kasa yake fada a wani taro saboda sunga zabe ya taho zasu baza kudi domin dan kasa ya manta ya zabe su, to yana kara zabensu  suka koma matsalarda za a koma ya fi na yanzu dan haka ya zama wajibi mutane su bude ido PDP itace mafita ita ya kamata a yi domin kowa yanzu a kasar nan ya ga al’kiblar da wadanda suke mulkin kasar a yanzu suka kai ta.

Exit mobile version