Ba Wani Gwamnan Da Ya Isa Ya Yi Babakere A Jam’iyyar PDP –Wike

Daga Umar A Hunkuyi

Gwamnan Jihar Ribas, Nyesom Wike, ya bayyana cewa, ba wani Gwamna da ya isa ya mamaye tsarin Jam’iyyar na su ta PDP, a matsayin kayansa, inda ya bayyana masu rade-radin hakan a matsayin makaryata.

Da yake magana a cikin wata tattaunawa ta musamman a gidan Talabijin na Channels, a karshen makon nan, Wike, ya bayyana daukacin gwamnonin Jam’iyyar ta PDP, da cewa duk matsayin su guda ne, suna kuma aiki ne domin ganin daidaiton Jam’iyyar.

Ya ce, ba wani Gwamnan da yake juya akalar Jam’iyyar a wata Jihar ta daban da ba ta shi ba.

Da yake mayar da martani a kan jawabin da aka ce tsohon Shugaban kasa, Olusegun Obasanjo, ya yi, Wike, ya ce, ai tsohon Shugaban ya rigaya ya bar Jam’iyyar ta PDP, har ma ya yaga katin zamansa dan Jam’iyyar, to don me kuma yake damuwa da abin da ke faruwa a Jam’iyyar ta PDP.

Gwamnan, ya yi nuni da cewa, ba kudi ne za su iya daidaita jam’iyyar ba, face dai hadin kan ‘ya’yanta.

Sannan ya ce, a irin wannan yanayin, hatta ma hukumar zabe ta kasa mai zaman kanta, (INEC), ta rasa kumajin iya shirya sahihin zabe.

Wike, ya ce, ba maganar fatan baki kadai ba, kamata ya yi hukumar zaben ta dauki kwararan matakan da za ta nu nawa ‘yan Nijeriya cewa,a shirye take da ta gudanar da sahihin zabe.

Abu na farko In ji Wike, ya wajaba hukumar zaben da ta yi bincike a sarari, ko su wane ne, shugabannin jam’iyyar APC, din da suka buga jabun takardun hukumar zaben na jabu a Jihar ta Ribas.

Sannan kuma,hukumar zaben ta INEC, ta bayyana ko ta yaya ne ‘yan sanda suka sami ingantaccen sakamakon zaben mai dauke da lamba iri daya na zaben shiyyar Dan majalisar Dattawan Ribas ta gabas, inda har hukumar zaben ta ayyana Sanata George Sekibo, a matsayin wanda ya lashe zaben, kafin daga bisani, mutane su zo da wani sakamakon zaben na daban, wanda Kotu ta yi amfani da shi ta tabbatar da dan takarar Jam’iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben.

Kan irin ayyukan da ya yi a Jihar ta Ribas, ya nanata cewa, yanzun su sun fito da wani tsari na kin barin ayyukan da ba a kammala ba, wadanda ya gada daga wanda ya gabace shi.

Ya kara da cewa, gwamnatin sa ta aiwatar da mahimman ayyuka a dukkanin Kananan hukumomi 23 na Jihar, sannan kuma duk ayyukan da ya gada daga Ameachi, ya kammala su.

“Na shirya yanda zan iya kammala duk aikin da na sanya a gaba ne a cikin shekaru hudu, ba zan fara wani aikin da na san ba zan iya kammalawa ba.”

Ya ce, “Gwamnati na, ta karfafa hanyoyin da za su kara kusanto da mata cikin gwamnati, da kuma tallafa masu. Mun kuma kebe sama da Naira milyan 500 domin tallafawa matan Jihar Ribas.”

Ya koka da cewa, ba a bi ta hanyar da ta dace ba, wajen sanar da shi ziyarar da Shugaban kasa zai kawo a Jihar na shi ta Ribas, yana mai cewa, ai a tsakaninsa da fadar ta Shugaban kasa, ya wuce a ce sanarwa ce kawai zai ji a jaridu ta bakin Femi Adesina.

“Idan an ce Shugaban kasan zai zo ne domin ya jajantawa iyalan mamatan ranar 1 ga watan Janairu ne, hakan yana da kyau. Domin ko a lokacin da abin ya faru a ranar 1 ga watan Janairu ba wanda ya jajantawa gwamnatin Jihar Ribas. A maimakon hakan ma, sai Shugabannin APC din suka saka siyasa a cikin lamarin.

Gwamnan ya ce, kusan shekaru uku kenan, ba wani abin da Jihar ta Ribas ta amfanu da shi daga gwamnatin APC ta tarayya, ya ce, maganar yashe yankin Ogoni, har gobe a matsayin mafarki yake, hakanan batun aikin hanyar Bodo zuwa Bonny, shi ma ana gab da yin watsi da shi.

Ya karfafa cewa, aikin hanyar Gabas maso kudu, da na Filin saukan Jirage na Fatakwal da sauran ayyukan gwamnatin tarayya a Jihar duk an yi watsi da su.

Exit mobile version