”Dan wasan gaban Bayern Munich Harry Kane ya bayyana cewar zamansa a Bayern Munich ya bude wani sabon Babi a rayuwarsa don haka a shirye yake ya bude tattaunawa da Bayern Munich kan yiwuwar saka hannu akan sabon kwantaragi, Kane ya shafe rabin shekarun kwantiraginsa a Bayern Munich, Kane ya saka hannu akan shekaru hudu da Bayern Munich wadda ta dauko shi daga Tottenham Hotspur kan fan miliyan 86.4 a shekarar 2023.
- Gwamnan Bauchi Ya Tabbatar Wa Sarakuna Ba Zai Rage Musu Iko Ba A Shirinsa Na Ƙirƙirar Sabbin Masarautu
- Tsaro: Gwamnan Kogi Ya Ayyana Yaƙi Da Haƙar Ma’adinai Ba Bisa Ka’ida Ba Da ‘Yan Bindiga
Dan wasan mai shekaru 32, ya zura kwallaye 103 a wasanni 106 da ya buga wa kungiyar ta Jamus, wanda ya taimaka mata lashe kofin Bundesliga na shekarar 2024-25 kofi na farko da ya dauka a tarihinsa na kwallon kafa, Kocin Tottenham Thomas Frank ya ce yana son ganin Kane ya koma Ingila, Kane na bukatar kwallaye 48 don kawar da tarihin da Alan Shearer ya kafa a tarihin gasar Fiimiya da kwallaye 260.
Sai dai kyaftin din na Ingila ya ce baya sha’awar komawa gida kamar yadda yakeyi a lokutan baya, inda yake tunanin tsawaita zamansa a Munich, Kane shi ne wanda ya fi kowa zura kwallo a raga a Tottenham da Ingila, kuma a kwanan baya ya zama dan wasa mafi sauri wajen jefa kwallaye 100 a raga a duka manyan gasannin Turai 5.
“Kafin in samu wani kofi bansan yadda ake ji ifan an lashe kofi ba, amma tun bayan lashe kofi na farko tareda Bayern Munich sai naji cewa ina bukatar lashe manyan kofuna da dama yanzu, hakan ya sa ba zanyi saurin barin wannan kungiya da na lashe kofin farko a cikinta ba, kofin ya kara min kwarin gwiwa na kara yin aiki da kyau, ina ganin na nuna hakan a bana” inji shi.