Connect with us

SIYASA

Ba Za A Ba Melaye Takara Kai Tsaye Ba –PDP

Published

on

Jamiyyar PDP reshen mazabar Kogi ta gabas ta yi shelar cewar,babu wani dantakara da zata baiwa tikitin takara kai tsaye a zaben kakar 2919.
Jamiyyar ta cimma wannan matsayar ce a ranar Lahadin data gabata a lokacin wata ganawa da ta yi da masu ruwa da tsaki da kuma shugabannin mazabar ta Kogi ta gabas.
Ganawar ta gudana ce a gidan Janar Dabid Jemibewon, mai ritaya dake Aiyetoro Gbedde wanda yana daya daga cikin wakikan kwamitin amintattu na jamiyyar.
Masu ruwa da tsakin, sun yanke shawarar cewar zasu yiwa dukkan ‘yan takarar adalci a lokacin zaben fitar da gwani na jamiyyar.
Acewar PDP, ta dauki matakin ne don amfanin jamiyyar don ta tabbatar da Bara dannewa ko wanne dantakara hakkinsa ba.
Har ila yau, PDP ta yi kira ga dukkan ‘yantakarar su kasance masu hali na gari su kuma zage wajen bin dokokin jamiyyar.
Ta kuma yi tir da zaben cike gurbi da hukumar zabe ta kasa INEC ta gudanar a mazabar Lokoja/Kogi ta tarayya, unda ta yi nuni da cewar, zaben abin kunya ne kuma bai cima sharudda ba.
Jimiyyar ta kuma koka a kan yadda aka nuna hakin dabar siyasa a lokacun gudanar da zaben, unda ta dora laifin hakan akan gwamnatin jihar akan yin amfani da ‘yan ta’addar siyasa da jami’an tsaro.
A karshe PDP ta yi kira ga gwamnatin tarayya data dauke kwararan matakai don kare sake aukuwar hakan a nan gaba, in kuma bats yi hakan ba, jama’a zasu dauki doka a hannunsu.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: