Zubairu T M Lawal" />

Ba Za A Samu Bambancin Siyasa A Majalisar Nasarawa Ba, Cewar Sabon Kakakin Majalisa

Kakakin Majalisar dokokin jihar Nasarawa,  Alhaji Ibrahim Balarabe Abdullahi, ya bayyana haka wajen bikin rantsar da su a zauren Majalisar ranar Litinin. Ibrahim Balarabe Abdullahi  ya yi nasarar komawa kan mukaminsa karo na biyu a Majalisar dokokin jihar.

An yi nasarar  rantsar da ‘yan Majalisar karo na shida, Majalisar ta sake zaben Ibrahim Balarabe Abdullahi, mai wakiltan mazabar Toto da Umksha a matsayin kakakin Majalisar, wannan ya ba shi damar jan ragamar Majalisar a karo na biyu.

Bayan Akawun Majalisar Mista. Ego Agawshi me Keffi, ya karanto dokokin Majalisar da kuma sharuddan zaben Shugabannin Majalisa. Sannan ya kirayo sunayen ‘yan Majalisa 24 da suka samu nasarar zama ‘yan Majalisar.

Hon. Muhammad Okoko, dan Majalisa mai wakiltar mazabar Udege Loko, shi ne ya zabo Hon. Ibrahim Balarabe Abdullahi, a matsayin Shugaban Majalisar. Sannan Hon.Aliyu Dogara Muhammad, mai wakiltar Wamba ya amince da zaben Ibrahim Balarabe Abdullahi, a matsayin Shugaba.

Hon. Ibrahim Muluku mai wakiltan Nasarawan Eggon   ya zabo Hon.Neyemiya  K. Dan Daura, a matsayin mataimakin Shugaban Majalisar. Shi ma Hon. Danladi Jatau, daga Kokona ya amince da zaben Dan Daura.

Duk cikansu sun bayyana wadanda aka zaban a matsayin kwararun da suka cancanta a zabe su. Sun bayyana irin dattakon Kakakin Majalisar Ibrahim Balarabe Abdullahi, kamar yanda ya jagorancin Majalisar a karon farko.

Bayan rantsar da Shugaban da mataimakinsa, Kakakin Majalisar ya rantsar da sauran ‘yan Majalisar 22.

Sanan ya yi kira gare su da su hada kai su yi aiki tare ban da la’akari da nuna bambancin jam’iyya. Ya kara da cewa, burinsu a Majalisa shi ne ciyar da jihar Nasarawa gaba.

Sannan ya ce, Majalisar za ta yi aiki da dukkanin bangarorin shari’a ba tare da son rai ba.

Ya ce, za su baiwa ma’aikatan shari’a da bangaren Gwamnati goyon baya wajen aiwatar da ayyukan ci gaban jihar Nasarawa.

Ya ce, kamar yanda muka wakilci al’umma za mu yi aikin da zai faranta masu rai. Ba za mu amince da dukkanin wani sabanin dokar da zai janyo cikas a jihar ba.

An dai rantsar da ‘yan Majalisar gaban dubban magoya bayan su da su ka yi masu rakiya

Exit mobile version