Shugaban rukunin kamfanin Dangote, Aliko Dangote ya bayyana cewa matatarsa ta na da isasshen man fetur domin biyan bukatar ‘yan Nijeriya, amma dole ne sai manyan ‘yan kasuwa sun dauki man domin rage wahalhalun da ake fama da su a yanzu.
Ɗangote ya bayyana hakan ne ga manema labarai a fadar shugaban kasa a ranar Talata tare da ministan kudi, Wale Edun a fadar shugaban kasa da ke Abuja.
“Muna iya bai wa ‘yan kasuwan lita miliyan 30 a kullum,” in ji Ɗangote , inda ya kara da cewa matatarsa ta tanadi lita miliyan 500 na man fetur. “Wannan ya isa a bai wa ‘yan kasuwa har na tsawon kwanaki 12 ba tare da an sake tace wani ba.”
Ya nanata cewa, shi ta ce mai yake yi, ba sayar da man ba a gidajen mai, don haka, ‘yan kasuwa ne ke da nauyin rarraba man zuwa gidajen mai.
“Idan ‘yan kasuwa suka sayi man, to ba za a yi wani layi a gidajen mai ba kwata-kwata.” In ji Ɗangote