Ba Za Mu Amince Da Cin Zarafin Mata Da Kananan Yara Ba —Bilkisu Ibrahim Suleman

Shugabar riko ta kungiyar lauyoyi mata reshen jihar Kano Hajiya Bilkisu Ibrahim Sulaiman ta bayyana cewar babbar maufar wannan kungiya ta su ta (FIDA) ita ce kokari wajen taimakawa al’umma musamman raunana da suka hada da mata gami da kananan yara. Bilkisu Ibrahim Sulaiman ta yi wannan jawabi ne jim kadan bayan kammala wani taro na karawa juna sani da kungiyar su ta lauyoyi mata ta duniya reshen jihar Kano ta gudanar a dakin taro na Gidan Mumbayya da ke cikin jihar Kano.

Bilkisu Ibrahim ta ci gaba da cewa, wannan kungiya ta lauyoyi mata ce zalla wacce ake yi wa lakabi da karshen  Turanci da International Federation of woman lawyers , FIDA, reshen jihar kano, daga cikin tsarinsu shi ne cewa suna yin yaki da cin zarafin mata da kananan yara da ke faruwa a cikin al’umma a halin yanzu duba da haka da ya sa taron da suka gudanar a yau ya fi mai da hankalinsa dungurungum a kan wannan matsala wadda ta hada da fyade da ake yi wa mata musamman yara mata kanana,ta kara da cewa wannan kungiya na kokarin jan hankalin al’umma kan cewa a daina cin zarafin mata da kannan yara saboda yin hakan na jawo matsaloli gami da gurbata tarbiya a cikin al’umma da muke rayuwa a cikinta.

Bilkisu ta ce kungiyarsu ta, (FIDA), ba za ta yarda da ganin cin zarafin mata da kananan yara yana ci gaba da gudana ba,sannan ta yi nuni da cewa suna yi kira da babbar murya ga al’umma su yi kokarin bi tarbiyyar da addinin Musulinci ya gina saboda yin hakan za a samu mafita bangaren gwamnati kuma ta ce wannan kungiya na rokon gwamnati da ta ci gaba da  karfafa hukumomi irin na Hisba domin su ci gaba da sasanta ma`aurata a kodayaushe. Shugabar ta yi nuni da cewa, ba za su bar kungiyoyi masu zaman kansu ba, saboda su ma suna da rawar da za su taka wajen cim ma wanna tsarina yaki da cin zarafin yara da mata, daga karshe ta yi amfani da wannan dama wajen kira ga iyayen yara da su mayar da hankalinsu sosai wajen tarbiyyar `ya `yansu musamman mata saboda a cewarta idan mace ta samu  kulawa tare da tarbiyyar to tamkar al’umma aka gina saboda mata su ne iyayen al’umma injita bangaren yada labarai kuwa Bilkisu ta ce kungiyar ta,(FIDA),tana matukar jin dadin irin gudummawar da suke bayarwa musamman wajen wayar da kan al’umma dake gudana a kan illar wannan matsala,tare da kokkrin da suke yi na kwarmata duk wanda aka samu da wannan dabi`a.

Exit mobile version