Ba Za Mu Bar ‘Yan Bindiga Su Sauya Rayuwar Jama’a Ba – Gwamnan Neja

Neja

Daga Mahdi M. Muhammad,

Gwamnan jihar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya bayyana cewa, ayyukan ‘yan bindiga a cikin jihar ba za su taba tsoratar da gwamnati ko jama’a ba saboda gwamnati ba za ta bar ‘yan bindiga su canja salon rayuwar mutane ba.

 

Gwamnan ya kafa hukumar yaki da ‘yan bindiga ta musamman (NSBC), wacce ta kunshi kungiyoyin ‘yan banga tara, gwamnan na ta fadi tashi wajen ganin ana magance matsalar ‘yan bindiga a jihar.

 

Da yake magana game da karuwar ayyukan ‘yan ta’addanci a jihar, Bello ya bayyana cewa, jihar ba za ta bari ‘yan bindiga su canja salon rayuwar mutane ba duk da cewa suna kokarin tilasta mutane su sauya salon rayuwarsu.

 

“‘Yan bindigar suna son tilasta mana mu canja salon rayuwarmu a jihar Neja amma ba za mu yarda da hakan ba. Sun hana yaranmu zuwa makaranta, sun hana mu tafiya a kan hanyoyinmu, sun hana manoma zuwa gonakinsu kuma yanzu haka suna kokarin hana ’ya’yanmu zuwa makarantar Islamiyya, amma ba za mu ji tsoro ba, kuma ba za mu bari hakan ta faru ba domin za mu ci gaba da rayuwa irin ta yau da kullum,” in ji shi.

 

Da yake kaddamar da ‘yan bangan na musamman a hedikwatar ‘yan sanda ta jihar a Minna, Gwamnan ya bayyana cewa, zai taimaka wajen takaita ayyukan matasa masu zaman banza a fadin jihar.

 

A cewar Gwamnan, gwamnatin jihar ce ta kirkiro da shawarar kafa kungiyar ta ‘Bigilante Corps’ ta musamman, sannan kwamishinan ‘yan sanda na jihar ya kara da cewa, za ta fadada ayyukan dukkanin tsaro na cikin jihar zuwa masu yi wa kasa hidima ta musamman.

 

Kungiyoyin da suka kasance cikin rundunar ta musamman sun hada da, Chinaka, ADC, Abidoka, WAI BRIGADE, Hunters Group, AOG, Bigilantes, Maito da Maitumbi Security Organisation.

 

Ya bayyana cewa, karuwar al’amuran kungiyoyin matasa masu zaman banza da ayyukansu a fazin jihar musamman babban birnin jihar ya zama ba karbabbe ba kuma suna bukatar tsauraran matakai.

 

“Yayin da hukumomin tsaro ke fada da ‘yan bindiga a yankunan karkara, wani sabon salo ya zo a Minna wanda ba za a yarda da shi ba. Muna da halin da muke ciki inda muke da kungiyoyin matasa masu fada da kansu, suna haifar da rauni a kan matafiya wanda sam ba za a yarda da shi ba,” in ji shi.

 

Sai dai Bello ya gargadi mambobin kungiyar ‘yan bangar na musamman da su yi aiki a cikin doka tare da jaddada cewa cin zarafin dan adam da zai karbu ba.

 

Kwamishinan ‘yan sanda na jihar, Adamu Usman ya ce, an horar da ‘yan banga na musamman har na tsawon makonni biyu kuma an koya musu yadda za su magance tashin hankalin matasa a Minna babban birnin jihar.

 

Usman ya yaba da tsarin da jihar Neja ta bi ta hanyar bai wa ‘yan sanda karfin horo da sa ido kan ayyukan ‘yan bangar.

 

Motocin Hilud guda goma, babura 20 tare da mambobi 161 an kaddamar dasu a matsayin kashi na daya a hukumar ‘yan bangar.

 

Gwamnatin ta bayyana cewa, kashi na biyu zai fara nan ba da jimawa ba kuma za a sake yin sa a wasu sassan jihar.

Exit mobile version