Dan wasan baya kuma kaftin din kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid, Sergio Ramos, ya bayyana cewa ba zasu fara maganar lashe gasar La ligar bana ba duk da cewa sun koma mataki na biyu akan teburin bayan da suka doke kungiyar Eibar da ci 3-1 a wasan mako na 14 a ranar Lahadi.
Dan wasa Karim Benzema ne ya fara ci wa Real Madrid kwallo a minti na shida da fara wasan, sannan minti bakwai tsakani Luka Modric ya kara ta biyu sai dai Eibar ta zare kwallo daya ne ta hannun Kike Garcia a minti na 28 da wasan.
Daf da za a tashi daga wasan ne Real Madrid ta kara ta uku ta hannun Lucas Bazkuez da hakan ya tabbatar mata da maki ukun da take bukata kuma cikin wasanni 14 da ta buga a bana ta yi nasara a guda tara da canjaras biyu da rashin nasara a karawa uku.
Haka kuma Real Madrid mai rike da kofin ta ci kwallo 25 aka zura mata 14 a raga, saura wasanni 24 a La Liga da ke gaban kungiyar a bana bugu da kari da wannan sakamakon Real Madrid ta koma ta biyu da maki 29 iri daya da na Atletico Madrid wadda ke jan ragamar teburin La Liga sai dai kafin karawar Real Madrid tana mataki na uku a kan teburi da maki 26, ita Eibar mai maki 15 tana ta 13 a kasan teburin gasar bana.
A kakar bara da kungiyoyin biyu suka fafata a La Liga:
Lahadi 14 ga watan Yunin 2019 Real Madrid 3 – 1 Eibar
Asabar 9 ga watan Nuwambar 2019 Eibar 0 – 4 Real Madrid
‘Yan wasan 22 da Zinedine Zidane ya je da su Eibar.
‘Yan wasan Real Madrid:
Masu tsaron raga: Courtois da Lunin da kuma Altube.
Masu tsaron baya: Carbajal da E. Militão da Sergio Ramos da R. Barane da Nacho da Marcelo da Odriozola da kuma F. Mendy.
Masu cin kwallaye: Benzema da Asensio da Lucas B. da Jobic da Mariano da kuma Rodrygo.