Ba Za Mu Kashe Kudi Da Yawa Ba A Kasuwar Siyan ’Yan Wasa –Mourinho

Mai koyar da yan wasan kungiyar kwallon kafa ta Manchester United, Jose Mourinho ya bayyana cewa kungiyar bazata kashe makudan kudade ba a kasuwar siye da siyar da yan wasa mai zuwa saboda kungiyar tanada matasan yan wasa.

Tun bayan komawarsa kungiyar, Mourinho ya kashe kudade dayawa wajen siyan yan wasa irinsu Paul Pogba da Rumelu Lukaku da Nemanja Matic da sauran yan wasan da kungiyar ta siya da tsada.

Mourinho yace zasu kashe kudi wajen kara karfin kungiyar amma ba kamar yadda ake tunani ba sannan saboda akwai matasan yan wasa a kungiyar da suke bukatar a basu dama domin suma su bawa kungiyar gudunmawa.

Manchester United dai tana kokarin ganin ta kawo yan wasan da zasu goga kafada da kafada da kungiyar Manchester City a kakar wasa mai zuwa bayan da City din ta lashe gasar firimiyar wannan kakar da tazarar kusan maki 16 duk da cewa saura wasanni 4 a kammala gasar.

Kungiyar kwallon kafa ta Arsenal zata ziyarci filin wasa na Old Trafford a ranar Lahadi mai zuwa a wasan firimiya kuma wasan da ake ganin shine na karshe a tsakanin Wenger da Mourinho bayan da mai koyar da yan wasan na Arsenal ya bayyana cewa zai bar aikin koyar da kungiyar a karshen wannan kakar.

 

Exit mobile version