Ba Za Mu Sayar Da Mbappe Ba – PSG

PSG

Shugaban kungiyar kwallon kafa ta Paris Saint Germain ta kasar Faransa, Nasser Al-Khelaifi ya kawo karshen duk wasu zantuka dake alakanta batun sayar da gwarzon dan wasan gaba na kungiyar, Kylian Mbappe.

Da yake shaidawa jaridar L’Ekuipe, Al-Khalifi yace, Mbappe zai ci gaba da kasancewa daram a babban birnin Faransa Paris, yana mai cewa, basu da niyyar sayar da Mbappe, hasalima dan wasan ba zai koma ko ‘ina a kyauta ba.

A watan Yuni shekarar 2022 ya kamata kwantiragin matashin dan wasa Mbappe ya kare, kuma ansha alakanta shi da komawa kungiyar kwallon kafa ta Real Madrid dake Spain sannan itama Liberpool tana bibiyarsa.

Barcelona bata da kudin sayen Neymar 

Har ila yau, shugaban na PSG yayi kuma tsokaci dangane da batun komawar dan wasa Neymar Junior zuwa Barcelona, inda ya ce kungiyar ta Catalonia bata da kudin sayen dan wasan a yanzu, hasalima dan wasan bashi da niyyar yiwa tsohowar kungiyar tasa kome.

Exit mobile version