Ba Za Mu Yi Kasa A Gwiwa Ba Wajen Kare Muradun Kasuwanci A Jihar Kano – Dandalama

Kasuwanci

Tare da Bashira A. Nakura, bushiranakura12@gmail.com, 08999263283:

 Ana yi wa Kano kirari da cibiyar kasuwanci, wannan ya sa ta zamo fintikau a harkar hada-hadar kasuwanci ba ma a Arewa ba har ma da Nijeriya bakidaya. Bisa wannan take da ake wa garin, muka tattauna da daya daga cikin masu kare muradun kasuwanci a jihar. Hirar a cike take da abubuwa masu tarin yawa na amfani. Ga yadda ta kaya.

Takaitaccen tarihinka?

 

Assalamu  alaikum. Sunana Abdullahi Musa Dandalama. An haife ni a garin Dandalama cikin karamar hukumar  Dawakin Tofa. Na yi primary na anan,  na fara karamar sakandire, anan, sannan na  na tafi Sokoto na yi karatu a Federal Secondary. Daga nan na tafi makarantar koyon aikin likitanci inda na karanci bangaren hakori ma’ana Dental Health Tehnicians. Daga nan na tafi kasar Masar  nayi karatun digiri. Yanzu haka Ina kan yin digiri  na biyu Insha Allahu.

 

Dan kasuwa ne kai ko ma’aikacin gwamnati?

 

Ban yi aikin gwamnati ba. Tun da na gama sakandire nake yin kasuwanci iri daban-daban. Na yi aikin kafinta abin da ya shafi  rufi da sauransu. Sannan ina noma wanda  muka gada iyaye da kakanni. Sannan na tafi Abuja neman kudi, anan kuma na shiga cikin harkar sadarwa.

 

Harkar sadarwar nan a cikinta muke har yanzu. Cikin ikon Allah sai Allah ya fado da mu cikin siyasa to yanzu ana yin abu biyu; siyasa da kasuwanci. Wannan shi ne a takaice.

 

Yaushe ka fara siyasa?

 

Na fara  siyasa ta dalilin ubanmu, shugabanmu Dr. Abdullahi Umar Ganduje tun lokacin yana mataimakin gwamna cikin shekarar 2012 muka fara Gwagwarmayar siyasa cikin ikon Allah.

 

To ga shi kusan ana iya cewa ka shiga siyasa da kafar dama domin har mukami kake da shi a wannan gwamnatin.

Mene ne matsayin mukamin naka. Kuma wacce irin gudunmawa kake ba wa matasa?

 

Alhamdulillahi naji dadin  wannan tambayar. Shi wannan mukamin da aka ba ni shi ne Babban  maitaimakawa zababben gwamnan Jihar Kano Dr. Abdullahi Umar Ganduje a fannin da ya shafi kananan ‘yan kasuwa masu sayar da kananan abubuwa walau a tituna walau a gida birni da  kauye  duka suna ciki, yanzu kokarin da muke yi mu tabbatar da wannan nauyin da aka dora mana shi ne domin wannan gwamnati ta kai ga gaci.

Gwamna na taimakon kananan yan kasuwa ta kowane fanni. Wannan ne yasa muka himmatu wajen daukar bayanai na masu kananan Kasuwanci. Akwai ofishinmu yana nan a Farm Center inda muke daukar jadawali da bayanai na dukkan masu kananan sana’oi, musamman yanzu mun fara da wadanda suke yin sana’a a tituna a fadin birnin Kano.

Ya zuwa yanzu mun dauki bayanai na matasa mun fara da shugabanninsu.  Da wannan bayanan ne  zamu tunkari gwamnati domin mununa mata yawan  matasa ‘yan kasuwa da muke da su.

Sannan wadannan mutane sai mu ba da shawara cewar ga abin da muke ganin ya dace gwamnati ta yi musu.

Duk da gwamnati yanzu ta sahale cewar akwai shirin da za ta gabatar wanda muke kira

Asibitin kasuwanci, watau business clinic  a turance.

Wannan shi muke so mu nunawa mutane  su inganta kuwancinsu a karkashin wannan shirin.

Munyi nisa wajen tattara bayanan mutane wadanda basu da rijista a gwamnatance, ta jiha ko ta kasa.

Muna kuma umartar mutane su je su yi rijistar kasuwancinsu ta yadda idan wani tagomashin gwamnati ya taso, zai kasance su ne a sahun gaba wajen samun amfani Insha Allahu.

 

Ta wacce hanya kuke bi wajen tattarawa da kuma tantance mutane masu aiwatar da kananan sana’oi?

 

Watau muna bin tsarin zakulo shugabanninsu da farko. Muna soma tattaunawa da su domin su yi mana bayanin irin matsalolin da kasuwancin nasu yake fuskanta.

Za su ba mu tarihin kasuwancin nasu da wuraren da suke aiwatar da shi.

Daga nan kuma sai mu nemi su ba mu sunayen membobinsu domin mu zauna da su mu ilmantar da su akan shirin mu na ‘Business Clinic’. Ko a kwanan nan ma, mun gana da wasu shugabannin kananan ‘yan kasuwa. Mun zauna da su tare da wakilan bankin Jaiz wanda ke duba yiwuwar ba wa ‘yan kasuwa rancen kudi kai tsaye. To daga cikin mutanen da muka yi tanadi, suna ta bude asusu da bankin na Jaiz, wadanda a baya ba su da shi, ana ba su rance daga dubu ashirin zuwa dubu hamsin ba tare da ruwa ba.

Sai bankin sun duba nau’in sana’ar mutum sannan su duba adadin kudin da za su ba shi. Wanda yake da muradi, yana iya zuwa ofishinmu da ke Farm center ya karbi form. Kuma cikin ikon Allah mutane suna ta zuwa suna fa’idantuwa.

Ayyukan da muka aiwatar suna da yawa, mun ilmantar da wasu ‘yan kasuwa.  Mun sa wasu yin rijista da hukumomin CAC da na Cooperatibe da sauransu.

Tun da kasancewar da ma Kano ita ce cibiyar kasuwanci, ba za mu kasa a gwiwa ba wajen ganin kasuwanci ya tsaya da kafafunsa bai mutu ba, ta kowacce hanyar da muke iyawa. Wannan shi ne muradin mai girma gwamnan jahar Kano Dr Abdullahi Umar Ganduje.

Da wannan muke sa ran zai rage radadin halin da mutane ke ciki ta hanyar inganta sana’oinsu domin ba za a iya samun aikin gwamnati ba a wannan yanayin da ake ciki na kuncin tattalin arziki ga kuma annobar Kwarona da abubuwan da ta hanyar na koma baya a fannin tattalin arziki.

 

A  maganar bashi, na ji ka yi batun babu ruwa a ciki. A baya kuma ka ambaci cewar jari kuke bayarwa kyauta. Ko me ya jawo zancen bashi kuma?

 

Ai  ba mu ne ke aiwatar da shirin  da bashin ba, bankin Jaiz ne da suka je jihar Katsina suka suma gabatar da shi.

Da muka ga yadda mutane suka fa’idantu, sai muka yi musu magana. Su kuma suka ce, idan muna bukata ana iya aiwatar da shirin a Kano. Ana kiran shirin da suna JAPEAK. Kuma bankin Jaiz ne ke aiwatar da shi domin ba da gudunmawa a Jihar Kano.

Gudunmawar kuwa ta shafi ilmantarwa da kuma bayar da bashi mara ruwa. ‘Yan kasuwa da dama sun samu ilimi, an duba sana’oinsu sannan an ba wa kananan ‘yan kasuwa bashi wanda da ma mu a bangaren kananan ‘yan kasuwar muke.

Su kuwa ‘yan kasuwa suna amfana ne da yadda suke aiwatar da kasuwancin, Idan aka ba wa mutum kamar dubu ashirin, zai cigaba da juya ta a hankali.

Za su bude masa akawun sannan a nuna masa yadda zai rika sa kudi kadan-kadan a ciki yana biyan bashin da aka ba shi har ya gama biya cikin lokacin da aka dibar masa. Wannan kenan.

Baya ga wannan kuma, muna aiwatar da shirin ne a kafafen yada labarai. Mun gano hanyar da gwamnatin tarayya za ta iya taimaka mana na rage radadin da jama’a ke ciki.

 

Daga lokacin da kuka soma aiwatar da shirin zuwa yanzu, ko za ka iya bayyana kungiyoyin da kuka taimakawa?

 

Gaskiya zuwa yanzu mun tantance kungiyoyi sun fi guda dari biyu wadanda suka hada da masu sayar da wayoyi da masu sayar cajoji da masu sayar da fuyawota da masu sayar da littattafai da kuma masu sayar da katin waya da sauransu.

Ban ji ka ambaci kungiyoyin mata ba a cikin tallafin?

To ai da yake yanzu muka fara. Abu na gaba a cikin jadawalinmu shi ne kungiyoyin mata masu kwalliya sannan kuma muna son mu fara bibiyar kauyuka, da ma suna da sana’arsu. Za mu neme su mu tattauna da su sannan mu dauki sunayensu da inda suke da lambobin wayarsu sannan mu nunawa gwamnati mu ga wanne irin yunkuri za a yi wajen taimaka musu. Muna da yakinin cewar idan muka tallafawa mata, su ma za su taimaki ‘ya’yan da suke raino.

Mata sun kasance koma baya a wajen samun tallafi, wannan ne dalilin da ya sa mai girma gwamna yake hobbasa wajen ganin cigabansu. Yayi umarnin cewar duk wani shiri da za a yi a rika shigar da mata ciki, domin su ne masu kula da yara. Ga wasu an sake su kuma an bar su da dawainiyar yara a hannunsu. Wasu kuma suna da mijin amma ba ya taimaka musu yadda ya kamata. Wasu mazan ma tsabagen mugunta ce da rashin tsoron Allah.

To don haka muke ganin cewar ya dace zawarawa wadanda aka sake su da wadanda aka mutu aka bar musu yara da ma wadanda nauyin iyalin ke wuyansu, a ba su fifiko, a basu jari da kuma nusar da su yadda za su yi da jarin da aka ba su.

Yanzu dai ba mu fara shiga kananan hukumomi ba tukunna, amma muna sa ran da yardar Allah bayan sallah za mu soma. Muna sa ran shiga kauyuka domin mu gana da masu sayar da kuli-kuli ne, masu man kuli, masu sai da gyada, masu sai da gishiri, da daddawa da sauransu.

Manufarmu, za mu tattara su duka mu tantance sannan mu tabbatar suna yin sana’ar da suka ambata. Sai mu shige gaba domin a tallafa musu. Mun lura sau da dama sai an tallafawa mutum da jari, sai kuma ya je ya aiwatar da wata hidimar da ba ta danganci abin da aka ba shi tallafi akai ba. Don haka muka yi tsarin wasu dabaru da za mu shigo da su yadda za mu tantance ko ana bin mutum bashi sannan mene ne silar durkushewar sana’ar tasa. Misali, a da yana juya kudin da suka kai dubu hamsin amma yanzu kayan da ke gabansa ba su wuce dubu goma ko biyar ba. Za mu bincika abin da ya jawo tabarbarewar kasuwancin nasa. Duk abin da muka gano su mu sa mutum a hanyar da in ba shi rance ko aro ko kuma tallafi daga gwamnati, zai yi amfani da shi wajen ganin ya cigaba da bunkasa kasuwancinsa ta yadda nan za mu yi alfahari da shi.

 

Yanzu ina son in tabbatar da maganar tallafin nan. Anya Kuna bayarwa ba wai kuna sa wa mutum rai ba ne, irin abin nan na ‘yan siyasa. Ku tara mutane domin cimma wata manufa ku dauki hotunansu, karshe ku bar su da hamma?

 

Hajiya har kin sa ni dariya. Ai babu maganar a tara mutane a bar su da hamma. Mu da muka san hakkin mutane kuma a ce ba a kai ga fa’idantuwa da abin da muka yi ba?

Abin da muke so shi ne, mutane su ba mu hadin kai domin abin nan da muke yi ba wai muna yin sa da kai ba ne. Kamar yadda na fada miki, majalisar jihar Kano ta sahale a aiwatar da Asibitin Kasuwanci. Wannan waje babban amfaninsa shi ne ilmantar da masu sana’a yadda za su inganta sana’arsu. Kowacce sana’a, muna zakulo kwararre, wanda yayi mata farin sani ciki da bai sannan mu zauna da shi tare da sauran masu sana’ar domin ya bayyana sirrin sana’ar da irin amfani da matsalolinta. Ba zai yiwu mu tara mutane muna ba su wahala alhali ba su fa’idantu da abin da muka yi ba. Wannan ba mai yiwuwa ba ne.

Idan a baya an yi abubuwa makamantan wannan da aka samu matsaloli, ba ma fata mu sake samun irin wannan matsalar yadda wasu suka soma gabatar da wani shirin kuma suka kasa tabbatar da shi ko kuma a karshe a wayi gari an yaudari mutane ne kurum. A tsarin jam’iyyar mu ta APC babu zancen yaudara. An kawo shirye-shirye masu yawa har da wanda shugaban kasa da kansa ya samar a karkashin bankin Nirsal. Wanda a ciki an ba wa mutane da yawa tallafi na miliyoyin kudi wadanda babu ruwa a ciki bisa zummar idan ka yi kasuwanci ka maida musu uwar kudin.

A yanzu haka, muna so mu nemi alfarma a wannan jihar ta Kano. Muna so mu nemawa mutane hanyoyin samun tallati a saukake. Ta yadda idan ka zo wajenmu muka saurari irin matsalolinka, za mu ba ka shawarwarin yadda za ka tafiyar da sana’arka kuma za ka fa’idantu kafin kuma abubuwan da za su biyo baya da iznin Allah.

 

.

 Bari mu koma baya. Kana dan kasuwa me ya ja hankalinka ka shiga siyasa?

 

Babban abin da ya ja hankalina ga sha’anin siyasa, mutane sai sun shiga siyasa ne za su iya ba da gudunmawa walau a unguwarsu ko jiharsu ko kuma kasarsu. Siyasa ce tsanin da za ka iya takawa har ka janyo na kasa da kai shi ma ya kai inda ka je ko ma ya wuce ka. Ta hanyar siyasa ne ake yin shugabancin dimokuradiyya. Kowanne dan kasa yana da ‘yancin fitowa takara a zabe shi ko ya zabi wanda yake so bisa ‘yancin da kundin tsarin mulkin kasa ya yi tanadi. Kana da damar ka yi duk jam’iyar da ta kwanta maka a rai. Mu dai tsarin jam’iyyar APC da ita muka fara kuma muka aminta da shi, kuma muka ga cewar idan Allah ya yarda mutane ba su ji kunya ba. Domin jadawalin alkawurra musamman wadanda mai girma Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi na cigaba da ayyukan da ya gada. Babu abin da za mu ce sai Alhamdulillahi, mun gani yayi abubuwa da dama wadanda aka fara su a baya aka bar su, ya zo ya dora akansu.

Wannan a takaice shi ya ja hankalina domin na shiga sahun mutanen da suke bada gudunmawarsu cikin al’ummarsu. Ta siyasa ne kadai ake iya samun wannan, kuma hakan bai sa mun ajiye kasuwancinmu ba. Saboda idan ka ce za ka ajiye kasuwancinka saboda sha’anin siyasa domin sa rai na wani takaitaccen lokaci, to fa mutum ya yi wa kansa kassasaba.

Idan da za mu bayar da shawara ga mai son shiga siyasa, za mu iya ba shi shawara yayi siyasa gwagwadon karfi sannan ya nemi sana’a iya karfi domin mutumcin mutum a yanzu shi ne a sanka akan abin da ka kwarance. Kuma a haka ne nake nusar da mutane da duk wadanda ke tare da ni.

Wannan shi ne makasudin shiga ta siyasa, sannan an duba, an ga na jajirce, sai aka kira ni aka ce mun ba ka bangaren kananan sana’oi irin wadanda ka saba da su. To wannan shi ne abin da ya burge ni.  Na karba da hannu bibbiyu kuma na godewa mai girma zababben gwamnan jihar Kano, Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da ya jawo ni, ya duba muhimmanci na, ba domin na fi wasu a jihar Kano iya kasuwanci ba, ba domin na fi kowa iya tafiyar da abubuwan da suka shafi kananan sana’oi ba, sai dai duba da cancanta ta. Ina mika godiya gare shi bisa haka.

 

 

Wane ne ubangidanka a siyasa?

A gaskiya ba ni da uban gidan da ya wuce Dr Abdullahi Umar Ganduje a siyasa.

 

Komai na rayuwa dama ce. Kana ganin wata rana idan dama ta fado hannunka, kana da burin tsayawa takara?

 

Ah gaskiya ba ni da sha’awar tsayawa takara akan kaina kowace iri ce.

 

To amma ka manta cewar al:umma su ne takara. Kada ka yi mamaki wata rana su nemi kayi musu jagora. Kenan idan suka bukaci haka ba za ka yi musu ba?

 

To idan al’umma suka bukaci haka, kuma na yi shawara da mutanen da suke fada a ji, suke da kima da martaba a idon mutane, kuma ni ma ina ganin martabarsu, idan suka yi umarnin na karba sai na bi umarninsu. Amma muddin ban samu shawara daga wani babba ba, ya ce tunda mutane suka bukaci hakan, ka je ka yi. Ni dai a karan kaina ba zan yi ba. Domin kuwa nauyi ne ake dorawa mutum wanda sai ka yi da gasken gaske kafin ka iya sauke shi.

Bugu da kari kuma, yanzu ne ake koyon abubuwa a siyasa. Saboda haka, ba zai yiwu a ce za a fito a jagoranci wani bangare a siyasance ba. Da wahala gaskiya. Domin ba ka koya ba ma ballantana ka iya tsara yadda za ka yi. Fatan da muke yi, shi ne Allah ya kai mu lokacin da muka koya muka iya abubuwa da yawa. A ce misali, a kaso dari na sha’anin mulki mun koyi kaso casa’in, to muna sa rai a wannan lokacin Insha Allahu muna iyawa. Ko dai mu umarci wani ya yi, ko kuma idan mun samu dama za mu iya amsawa a lokacin amma ba yanzu ba.

Me za ka ce dangane da bullowar cutar annobar Kwarona, kasancewar komai ya ja baya har ana tunanin ta yi awon gaba da kaso mai tsoka na tattalin arzikin kasar nan? Ko za mu iya sanin barnar da ta yi a bangaren ku?

 

Gaskiyar lamari, kasa ta girgiza da bullowar annobar Cobid-19, domin kuwa ta haifar da matsaloli masu dumbin yawa. Matsalolin sun hada da rugurgujewar tattalin arziki na kasa walau na jiha, babu wani dan kasuwa da zai ce rugurgujewar tattalin arzikin ba ta shafe shi ba. Domin kuwa, an wayi gari ba ka isa la fita koda kofar gida ba. Hatta Sallah ma cewa aka yi ka yi ta a cikin gida ka saboda cutar Kwarona. Ta janyo fita ma ta gagara ballantana mutane su samu damar juya abin da ke hannunsu suna samun na batarwa. Sai da ta kai mutane sun cinye abin da ke hannunsu sun shiga maula. Har sai da ta kai mutane ba sa iya daga waya domin sau da dama kiraye-kirayen sha’ani ne na roko da maula alhali kai din ma baka da shi. Komai ya kare, sai abubuwa suka gagara. Gaskiya an sha wahala. Amma yanzu cikin ikon Allah abubuwa na farfadowa, sai dai mun ji an ce cutar Kwaron din ta sake bayyana, sai dai mu yi addu’ar Allah ya kawo mana sauki.

A gaskiya babu wani dan kasuwar da bai jigata ba. Na bangaren mu abin ya fi kamari, domin muna da wadanda ke talla a tituna, sai ka fito za su ganka su yi maka talla. To ba ka fita ba, su ma basu fita ba. Muna da mutanen da sai sun fito kasuwa sun bude sannan su samu abin da za su ci a wannan ranar. Alal hakika an shiga rigingimu da yawa ta dalilin Kwarona. Fatan da muke, Allah ya kawo mana karshen ta.

 

Wane fata gare ka kan Jihar Kano?

Babban fatan da nake yi wa jihar Kano, ta samu cikakkiyar martaba. Ta cigaba da zama jihar da tun tale-tale take matsayin cibiyar kasuwanci. Mu kara dagewa, matasanmu su tashi tsaye.

Fatan da nake ga matasanmu na jihar Kano, kada su zauna haka, don suna ganin sun yi karatun zamani su ce ba za su kasuwanci ba, wannan kuwa tamkar mutum ya mai da kansa baya ne. A rika taba kasuwanci, idan aiki ya samu, to falillahil hamdu kayi.

Idan kana kasuwa, Allah ya taimake ka , sai ka ga ita kadai ma ta ishe ka. Domin jihar Kano, jiha ce mai albarka. Fatan da muke yi Allah ya cigaba da bamu albarka. Wannan rashin tsaro da ake fama da shi, wanda ba iyakar jihar Kano ba ne, Allah ya kawo mana dauko. Kuma yawaitar satar mutane da ake yi da tashe-tashen hankula, muna rokon Allah yayi mana maganin su, ya kawo mana sauki. Allah ya cigaba da tallafa mana, ya saukar mana da albarka da alherai jihar Kano.

 

 

Wane fata za ka yi wa jaridar leadership?

Fatana ga jaridar leadership Allah ya kara yi musu jagora, ya amintra da su. Ya karawa jaridunsu farin jini da daukaka. Maaikatansu Allah ya sa su yi ta samun cigaba a rayuwarsu.

Allahumma amin

Bishira A. Nakura

Exit mobile version