Ibrahim Muhammad" />

Ba Za Mu Zura Ido Kannywood Ta Wargaje Ba – Gwamna Ganduje

Gwamnan Jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa, gwamnatinsa ba za ta zuba ido hakan nan masana’antar shirya Finafinan Hausa ta Kannywood ta rushe ba.
Kazalika, ya kara da cewa, ya na da kyakkyawan fatan wannan masana’anta za ta rika samar da shirye-shirye masu inganci da kuma ma’ana ta yadda za su yi daidai da al’adun al’ummar Jihar Kano bakidaya.
Gwamnan ya furta wadannan kalamai ne, yayin da ya kai ziyara ofishin sakataren Hukumar tace Finafinai ta Jihar Kano a kwanakin baya domin ganin yadda ta ke kasancewa a bangaren da ya shafi tantancewar da a ke yi wa ‘ya’yan kungiyar na Kannywood.
Har ila yau, Gwamna Ganduje ya cigaba da cewa, “yana da matukar kyau da kuma amfani a kara fadada wannan Masana’anta, ta zama wata katafariyar Jami’a a wannan Jiha. Haka nan, ba za mu taba lamuncewa da barin wannan Masana’anta ta mutu ba, domin kuwa tana da matukar muhimmanci a wajenmu. A yanzu haka, muna kan aikinmu na kara inganta Gidan Talabijin na ART da kuma Gidan Rediyon Kano, tare da kokarin inganta madaba’ar Jaridar Triumph”, in ji shi.
Don haka in ji Gwamnan, babu yadda za a yi a bar wannan Masana’anta ta Kannywood haka, ba tare da an inganta ta ba, “sannan za mu mayar da hankali kwarai da gaske tare da dora ta kan tafarki, wanda zai yi daidai da Addininmu na Musulunci da kuma sauran al’adunmu na Jihar Kano.
Har wa yau, “abin da ‘ya’yan wannan Masana’ata ke bukata a halin yanzu na farko, bai wuce a fara ba su horo na musamman da kuma tallafi ba. Saboda haka, Gwamnati za ta cigaba da yin iyakar kokarinta wajen sama wa ‘ya’yan Masana’antar ingantattun na’urori, wanda suka yi daidai da zamani”, a cewar ta Ganduje.
Ya kara da cewa, “a farkon lokacin da muka samu kanmu a kan karagar mulkin wannan Jiha, wannan Hukumar ta tace Fina-finai, kusan kawai suna ce a takarda, amma babu wani ayyukanta da take aiwatar yadda ya kamata, wannan dalili ne ya sanya muka ga dacewar zamanantar da ita, domin baiwa Addininmu da kuma al’adunmu muhimmancin gaske.”
Haka nan, ita ma a nata bangaren, Sakatariyar Ma’aikatar Yada Labara ta Jihar Kano, Hajiya Hafsat Iliyasu Aliyu, a yayin gudanar da wannan taro, ta bayyana cewa ko shakka babu Gwamnati, na baiwa wannan Ma’aikata dukkanin irin goyon bayan da ya dace.
Don haka a cewar tata, kamar yadda Mai girma Gwamna ya bayar da umarnin zamanantar da Gidan Talabijin na ART da na Rediyon Kano, ina tabbatar da cewa, a yanzu haka dukkaninsu, za a iya kalla da sauraronsu a wadansu daga cikin makwabtan kasashe kamar; Kamaru, Ghana da kuma Jamhuriyar Nijar.
A yayin da yake gabatar da nasa jawabin, Babban Sakataren Hukumar tace Fina-finai na Jihar Kano, Alhaji Isma’ila Na’abba Afakallah, cewa ya yi, an shirya wannan tantancewa ne domin kokarin hada kan ‘ya’yan wannan kungiya, tare da samar da cigaba ta hanyar bunkasa aikin wannan Masana’anta da kuma inganta ta.
Haka zalika, “yau ita ce rana ta karshe da ake gabatar da wannan horaswa, wadda a halin yanzu ‘ya’yan Masana’antar da suke da shaida da kuma lasisi, su ne kadai za su iya samar da waka ko shirya Fina-finai a wannan Masana’anta. Saboda haka, muna fatan wannan zai kasance a matsayin ginshiki na farko da zai samar da gyara a cikin wannan Masana’anta ta Kannywood”, in Afakallahu.
Haka nan shi ma a nasa bangaren, Jarumi kuma mashiryin Fim Nura Hussaini, ya yi jawabi a maimakon sauran ‘ya’yan wannan Masana’anta ta Kannywood, inda ya ce Gwamna Ganduje shi ne Gwamna na farko da aka taba samu a Jihar Kano, da ya halarci taron da ya shafi wannan Masana’anta tasu. Saboda haka, suna yi masa godiya tare da nuna matukar farin cikinsu da jin dadi, ganin yadda Gwamnan yake nuna damuwarsa da kuma tsananin kauna a gare su, in ji Hussaini.

Exit mobile version