Connect with us

KASUWANCI

Ba Zai Yiwu A Sami Tsayayyar Hasken Lantarki Ba Har Sai A 2023 – Kamfanin Discos

Published

on

Kamfanonin da ke aikin raba hasken lantarki sun ce, kasarnan ba za ta iya cimma manufarta ba ta samar da wadataccen hasken lantarki a nan da shekaru biyar masu zuwa, matukar dai ba a iya magance matsalolin da ke fuskantar sashen samar da hasken lantarkin ba.

Kamfanonin sun bayyana hakan ne ta bakin babban daraktan su na bincike, Mista Sunday Oduntan, a wajen wani taron manema labarai da suka yi a Legas, ranar Talata.

Oduntan ya bayyana matsalar daidaita farashi a matsayin babban matsalar da ke damun sashen, inda ya yi nu ni da cewa, akwai bukatar gwamnati ta sanya farashin da zai dace da lamarin.

Ya ce, “Akwai bukatar samar da hadin kai a tsakanin masu ruwa da tsaki na sashen, domin su samar da tsayayyar mafita. Mu a shirye muke a kowane lokaci in an neme mu domin tattaunawa kan hakan, domin mun san aikin namu yana cikin hatsari ne. wannan yana da mahimmanci sosai a garemu bakidaya, domin matukar kamfanonin namu suka suka tsaya, tabbas bankunan kasarnan masu yawa duk za su tsaya ne su ma.

“In ma ba ku sani ba ne, a lokacin da suke sayar da hannayen jarin, kamfanin raba hasken lantarkin guda daya ne kadai yake da masu zuba jari kai tsaye daga waje, amma duk sauran ranto kudade ne suka yi daga bankunanmu na nan cikin gida, suna kuma biya ne da dala.”

Kakakin masu raba hasken lantarkin yana mayar da amsa ne ga bayanan da Ministan Hasken lantarki, ayyuka da gidaje, Babatunde Fashola ya yi, ya kara da cewa, “Sam bai kamata mu rika sanya siyasa a cikin sashen na samar da hasken lantarkin ba. Ina kuma bukatar ‘yan Nijeriya da su binciki duk abubuwan da muka fada su gani gaskiya muke fadi ko kuma karya ce muke yi masu. Ban ga dalilin da zai sanya mu yi karya ba. Domin in har akwai wadatattar hasken lantarkin da za mu raba, to ai a lokacin ne za mu sami kudi sosai.

“Ya kamata duk mu hada hannu ne wajen warware matsalolin da ke yi wa sashen tarnaki, in mun yi hakan, kowa zai ji dadi, masu amfani ma da hasken lantarkin duk za su ji dadi.

Ya ce, an siyasantar da maganan saka mitoci, duk da yadda kamfanonin raba hasken lantarkin suka nu na aniyarsu ta baiwa shirin goyon baya.

Oduntan ya kara da cewa, “Maganan mita a yanzun ba shi a hannun kamfanonin da ke raba hasken lantarkin na kasarnan. Mai lura da maganan daga ma’aikatar hasken lantarkin, ayyuka da gidaje, yanzun su suke daukan nauyin lamarin.

“Sune yanzun suke gaya mana abin da ya kamata mu yi, kuma a shiye muke mu ba su goyon baya don ganin samun nasarar shirin.

Kakakin kungiyar ya ce, samar da mitocin ga masu amfani da hasken lantarkin zai magance matsalar tsawwala wa masu amfani da lantarkin kudi.

Ya ce, “Amma kar mu kasa fahimtar lamarin, saboda na tuna mai girma Minista ya shawarce mu da mu je mu sanya wa mutane mita. Kila kuma ya manta ne da cewa, ai ya cire mu daga wannan aikin, wannan kuma ai aikin kamfanin da ya baiwa ne.

Advertisement

labarai