Connect with us

JAKAR MAGORI

Ba Zama Sai Mun Tabbatar Da Tsaro Ya Inganta – Buratai

Published

on

Shugaban Rundunar sojin Nijeriya, Laftanar Janar Yusuf Tukur Buratai, ya shaida wa dakarun sojin kasar cewa za su ci gaba da tsayuwa wurin yakar rashin tsaro a kasar nan har sai sun ga bayan ‘yan ta’adda da masu ta da kayar baya.

Buratai ya samu wakilcin laftanal janar Lamidi Adeosun a yayin bikin yaye sojoji karo na 79 a Zaria a ranar Asabar. Shugaban rundunar sojin ya jajanta cewa Nijeriya na fuskantar matsalar Boko Haram, ‘yan bindiga, masu garkuwa da mutane da sauran miyagun ayyuka da ke matsantawa rayuwa. Buratai ya taya sojojin murna tare da basu shawarar aiki tukuru, kwarin gwiwa, ladabi da nagarta.

“Ina so in sanar da cewa za mu ci gaba da yakar rashin tsaron da ya addabi kasar nan,” ya ce. ” Ana sa ran za ku saka duk wani kwarin gwiwarku wajen tabbatar da kun yi aiki cike da kwarewa. “Ina kira gareku da ku mayar da horarwa da kuka samu ta zamo jikinku a duk inda kuka samu kanku.” Ya ce rundunar sojin ta ba bai wa dakarun abin da ya kamata sannan tana sanya ran za su yi iyakar kokarinsu a yayin ayyukansu.

“Akwai bukatar ku sani cewa, a yau an kara karfin rundunar sojin Nijeriya saboda sun samu karuwar dakaru 4,918,” ya ce. “Ina tabbatar muku da cewa kun samu goyon baya daga wurinmu da kuma walwala mai dorewa.”

Advertisement

labarai