Ba zamu ƙara zaɓar Buhari Ba -Mai Rice

Daga Abdullahi Mauhammad Shaa, Kano

A madadin talakawan jihar Kano ranka ta kaf muna miƙa godiyar mu ga Goggo mai ɗakin Dakta Abdullahi Umar Ganduje, sannan muna addu’ar shekara ta 2019 ke ce first lady a ƙasar nan, wannan bayani ya fito daga bakin ɗan gwagwarmaya Alhaji Umar mai Rice jim kaɗan bayan isowar tawagar gwamnoni goma sha ɗaya waɗanda suka iso Kano a makon jiya domin shaida baicon ‘yan Gwamnan Kano Dakta Abdullahi Ganduje da kuma ɗan Gwamnan Jihar Ogun. Umar Mai Rice yace muna roƙon gwanonin nan shekara ta 2019 ku tsayar mana da Dakta Abdullahi Umar Ganduje takarar shugabancin ƙasarnan domin shi yafi kowa cancanta.

Da aka tambayeshi waɗannan gwamnonin yake magana sai ya amsa da cewar waɗannan gwamnonin goma sha ɗaya, ya ce kowanne ɗaya daga cikinsu yana da aboki guda daga cikin sauran gwamnonin, kenan tun daga nan muna da gwamnoni ashirin da biyu. Sharfuddeen Kantin Kwari ya ci gaba da cewa  ya ce mu talakawan Jihar Kano musamman ‘yan kasuwa ba zamu sake zaɓar Buhari ba ashekara ta 2019. Da aka tambayeshe baya ganin gwamnatin tasu tana can tana tattaunawa da shugaban ƙasar zai shigo Kano domin buɗe wasu manyan ayyuka? Sai ya amsa da cewa wannan zuwa bai dame mu ba duk gwamnonin ƙasarnan ba wanda ya kai Ganduje ayyukan alhairi, saboda haka yanzu ƙasa Ganduje ta tuna shi ake buƙata. Mu dai ko an tsaida Buhari a shekara ta 2019 ba zamu zaɓe shi ba.

Ya ci gaba cewa duk wani ɗan kayi nayi dake gindin shugaban ƙasa Buhari da yazo Kano ya nuna mana wani masallachi guda da Buhari ya baiw buta ko tabarma karauni ko ya bayar da gwangwanin alwala, na rantse zan raba gidan gonata biyu na bashi rabi, muna ji ana cewa Allah ya sa shinkafa tafi ƙarfin talaka, shekara ta 2019 bamu da wani ɗan takara a shekara ta 2019 a Nijeriya sai Dakta Abdullahi Umar Ganduje, inji Alhaji Umar mai rice.

Exit mobile version