Ba Zamu Tura ‘Yan Hidimar Kasa Yankunan Da Ake Da Matsalar Tsaro Ba – NYSC

NYSC

Hukumar da ke kula da masu hidimtawa kasa (NYSC) ta ce ba za ta tura ‘yan hidimar kasar zuwa yankunan da ake fama da matsalar tsaro ba, don su yi aikin malaman zabe na wucin gadi, musamman da yake an fi samu matsaloli a zabukkan gwamna da na ‘yan majalisar jiha.

Darektar yada labarai da hulda da jama’a ta hukumar, Misis Adenike Adeyemi ce ta bayyana hakan ga manema labarai, a yayin da take ganawa da su a ofishin hukumar dake Abuja, a yau Asabar, a shirye-shirye da hukumar take yi don fuskantar zabukkan gwamna da na ‘yan majalisun jiha da za a gudanar a ranar 9 ga watan Maris din nan da muke ciki.

Adeyemi ta bayyana cewa ba dan hidimar kasan da ya rasa ransa, a zabukkan shugaban kasa da na ‘yan majalisun tarayya da aka gudanar makon da ya gabata, inda ta kara jadadda anniyar hukumar wajen ganin ta kare rayuwar ‘yan hidimar kasar a koda yaushe, dan haka ne ma suka dauki matakin daina tura ‘yan hidimar kasar zuwa yankunan da ake da fargabar rashin zaman lafiya.

Duk an samu rikice-rikice a wasu yankunan kasar nan a lokacin zaben, amma dai babu dan hidimar kasa da rikicin ya shafa, domin an dau matakin kare lafiya da rayukan ‘yan hidimar kasar yadda ya dace, hukumar ta shaida cewa kiyaye lafiyar ‘yan hidimar kasar yana da matukar muhimmanci gareta, don haka ne ma ya sa bata tura su zuwa ga wuraren da ake samun rikici ko barazanar samun rikicin.

 

Exit mobile version