Connect with us

LABARAI

Ba Zan Bar Jam’iyyar PDP Ba Ko Ban Samu Takara ba–Lamido

Published

on

Tsohon gwamnar Jihar Jigawa kuma dan takarar shugabancin kasa a karkashin tutar jam’iyyar PDP, Alhaji Sule Lamido ya ce, ba zai bar jam’iyyar PDP ba ko da  bai samu cin zaban fidda gwani na dan takarar shugabancin kasa ba. Lamido ya fadi hakan ne lokacin da yake zantawa da manema labarai a gidan Janar Jeremiah Useni, yayin da ya kai masa ziyara ranar Laraba a gidansa dake garin Jos. Kafar yada labaran NAN sun ruwaito cewa Lamido ya kai ziyara zuwa sakatariyar jam’iyyan na PDP a jihar Filato inda ya bayyana aniyarsa ta tsayawa takaran shugabancin kasar nan a shekarar 2019.

“Dukkaninmu da muka fito takara a jam’iyyar PDP, dukkan mu daya ne kuma za mu iya mulkin Nijeriya.

“Shugabancin Nijeriya a shekarar 2019 ba wai kawai don ni kadai ba ne, dukkaninmu muna aiki kafada da kafada domin mu ceto kasar nan. Haka nan kuma in dai ban samu nasarar cin zaben fidda gwani ba to zan mara wa duk wanda ya yi nasara a cikin wannan jam’iyyan tamu mai albarka wato PDP.”

Dan takarar shugabancin kasar ya ba da tabbacin cewa jam’iyya za ta yi nasara. Lamido ya karyata jita-jitan da ake yi na cewa tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ne yake daukan nauyinsa a kan wannan takaran da yake yi. Ya kara da cewa bai da wani ubangida a cikin siyasa kuma ya fito wannan takara ne na shugabancin kasa don kashin kansa.

Tun da farko shugaban jam’iyyar na jihar, Mista Damishi Sango, ya tabatar wa dan takarar goyon bayan jihar, ya kuma shawarce shi daya yi kokarin ya doke sauran ‘yan takatarar dake neman jam’iyyar ta mika musu tikitin takarar a jam’iyyar.
Advertisement

labarai

%d bloggers like this: