Dan wasan Liberpool na gaba, Sadio Mane ya ce ba zai sauya salon yadda yake buga wasa ba duk da yadda kocin kungiyar, Jürgen Klopp ke goya masa baya wajen kare zarge-zargen da ake yi masa na faduwar da yake yi domin neman fanareti.
An dai ja wa Mane mai shekara 27, kunne a minti na 37 na wasan da suka taka daAston Billa inda aka tashi 2-1, ranar Asabar sakamakon faduwa da yayi ya nemi alkalin wasa ya bashi bugun fanareti.
Hakan ne ya sa kociyan kungiyar k wallon kafa ta Manchester City, Pep Guardiola ya fito ya bayyana cewa ‘yan wasan Liberpool za su iya iya faduwa domin su samu nasarar fanareti kuma sun dade sunayin hakan.
“Ba zan taba sauya salon yadda nake buga wasa ba saboda idan har na canja hakan yana nufin zargin da akeyi akaina ya zama gasjiya na cewa inayin lambo domin a bawa kungiya ta bugun Fanareti.” In ji Mane
Ya cigaba da cewa “An samu taho-mu-gama a wasanmu da Aston Billa kuma watakila ba fanareti ba ne kuma bai bayar ba sannan kuma ya ba ni katin gargadi amma zancen gaskiya ba ni da matsala da wannan batu.”
Kocin Liberpool din, Jurgen Klopp ya kare Mane inda yake fadin cewa Sadio ba mai faduwa ba ne kuma an samu yanayi ne a wasansu da Aston Billa inda ya yi kacibis da wani har ya fadi, tana iya yiwuwa ba fanareti ba ne amma dai ya yi taho mu-gama ba wai ya tsallake kafar wani ba ce ya fadi.”
Mane ya yi barkwanci inda ya ce idan ya sake samun wata damar irin wannan to zai sake kwanciya domin neman fanareti sai dai tuni masana wasanni sukayi kira ga alkalan wasa akan cewa su kula da yadda dan wasan yake buga kwallo.