Abba Ibrahim Wada" />

Ba Zan Gayyaci Sababbin ’Yan Wasa Ba – Kociyan Super Eagles

Kociyan tawagar Super Eagles ta Najeriya, Gernot Rohr, ya ce babu wani sabon dan wasa da zai gayyata domin wasan neman tikitin shiga gasar cin Kofin Afirka na shekara ta 2021 da tawagar za ta kara da jamhuriyar Benin da kuma Lesotho a wata mai zuwa.

Da yake hira da manema labararai kuma aka watsa a shafin YouTube na kungiyar, bayan dawowarsa Najeriya ranar Litinin, Rohr ya karyata rahotannin kafofin yada labarai na cewa hukumar kwallon kafa ta duniya FIFA ta baiwa wasu sababbin ‘yan wasa izinin buga wa Najeriya kwallo.

Kocin dan kasar Fransa da Jamus ya dage kan cewa yana da kwararrun ‘yan wasa a hannun sa kuma ba zai yi tunanin kawo wani sabon dan wasa ba a yanzu, yayin da’ yan wasan ke shirin wasan karshe na wasan neman cancantar shiga gasar cin kofin kasashen Afirka ta shekarar 2021.

Super Eagles, wadanda ke saman teburin rukunin L da maki takwas a wasanni hudu, za ta kara da kasar Benin a waje ranar 22 ga watan Maris, kafin ta karbi bakuncin tawagar ‘yan wasan kasar Lesotho ranar 30 ga watan Maris.

 

Exit mobile version