Umar A Hunkuyi" />

Ba Zan Goya Wa Kowane Dantakara Baya Baya Ba A 2019 –Al-Makura

Gwamnan Jihar Nasarawa, Umaru Tanko Al-Makura, ya ce ba wani dan takarar da yake neman ya gaje shi da zai marawa baya a babban zaben 2019.

Gwamnan ya bayyana haka ne ranar Asabar sa’ilin da manyan sakatarorin Jihar da shugabannin kananan hukumomin Jihar 13 suka kai ma shi ziyarar barka da Sallah a garin Lafiya.

Ya ce, duk da cewa ba dan takarar da zai goya wa baya, amma dai Jihar tana da bukatar jajirtaccen jagoran da zai dasa ne daga inda aka tsaya.

“Don haka za mu tantance sannan mu darje, domin mu tabbatar da mun dora wanda zai ci gaba da aiki ne daga inda muka kwana, ya kuma kawo zaman lafiya da ci gaban Jihar namu.”

Gwamnan kuma ya ja kunnen Shugabannin na Kananan Hukumomi da su kasance masu takatsantsan wajen alkinta dan abin da suke da shi a hannun su a kananan hukumomin na su.

Ya bayyana cewa, Jihar ta Nasarawa a karkashin jagorancin na shi, ta gabatar da zabukan kananan hukumomi har karo na biyu, a shekaru bakwai da ya yi na mulkinsa.

“Muna cikin Jihohi kadan a kasarnan da suka gudanar da zabukan kananan hukumomi har sau biyu.

Sannan ya yi alkawarin amfani da sauran abin da ya rage ma shi na mulkan Jihar wajen kyautata rayuwar al’ummar Jihar.

Tun da farko, Shugaban karamar hukumar Lafiya, Aminu Maifata, da ya yi magana da yawun takwarorin na shi, ya bayyana godiyarsu ne ga gwamnan a matsayinsa na jagoran Jam’iyyar ta APC a Jihar, saboda daman da ya ba su na yi wa Jihar hidima.

Ya kuma yi alkawarin nuna wa al’ummunsu ayyukan ci gaban da gwamnan ya kawo masu a yankunan na su.

Ya kuma yi roko ga gwamnan da ya amsa kiran da mutane ke yi masu da ya yarda ya amsa tsayawa takarar kujerar Majalisar Dattawa a shiyyar Nasarawa ta Kudu a zaben 2019.

Exit mobile version