Ba Zan Iya Lissafa Mutanen Da Na Kashe A Shekara Daya Ba – Wanda A Ke Zargi

Wani wanda a ke zargin mai garkuwa da mutane ne, Sani Haruna, wanda a ke yi wa lakabi da Gayu, wanda tawagar ‘yan sanda su ka samu nasarar cafke shi ranar Asabar, ya bayyana wa manema labarai cewa, ba zai iya lissafa mutanan da ya kashe a cikin shekara daya ba, wadanda su ka yi garkuwa da su, sannan su ka kasa biyan kudin fansa. Sani Haruna ya na daya daga cikin wadanda su ka yi garkuwa da Sheik Ahmad Sulaiman da kuma sauran mutane, ya fadi hakan ne lokacin da manema labarai su ke zantawa da shi a wani wuri inda a ka ijiye shi a garin Abuja. Matashin mai shekaru 20, ya na da yara guda biyu, ya bayyana cewa, ba ya cikin wadanda su ke sace mutane, amma ya na cikin wadanda su ke tsare wadanda a ka yi garkuwa da su.

Ya ce, shi ne ya ke kashe duk wanda a ka kasa biyan kudin fansan da mai gidansu ya nema a biya. Ya kara da cewa, tun da ya na cikin wadanda su ke tsare wanda a ka yi garkuwa da su, sannan kuma shi ne ya ke kashe wanda a ka kasa biyan masa kudin fansa, mai gidansa ya koya masa yadda a ke sarrafa bindiga, musamma ma kirar AK-47 wanda ya zaba a matsayin makami wacce ya ke amfani da ita wajen yin garkuwa da mutane. Sani Haruna ya bukaci gwamnatin tarayya da ta ba shi dama na biyu ya shiga cikin ‘yan sanda, wajen fatattakar ‘yan bindigar Katsina, Zamfara, babban hanyar Kaduna zuwa Abuja da kuma sauran yakunan kasar nan.

“Sunana Sani Haruna. Ina cikin masu gadin wadanda a ka yi garkuwa da su, wadanda a ka ijiye a dajin Jihar Katsina. Na kai tsawan shekara daya ina wannan aiki. Kafin in shiga wannan harkar, ina gudanar da sana’ar kiyo. Daga wajen kiwo ne, wani kwamanta ya gayyace ni zuwa tsare wadanda a ka yi garkuwa da su. Ya ce, ya shiga cikin wannan aikin ne tun lokacin da ya rasa shanunsa, inda ya nemi kwamantan ya sama masa aikin yi. Haruna ya kara da cewa, an koya masa yadda zai sarrafa bindiga, an ba shi inifom din sojoji a matsayin sa na mai gadin wadanda a ka yi garkuwa da shi. Ba zan iya lissafa mutanan da na kashe a cikin shekara daya ba, tun lokacin da na fara yin garkuwa da mutane.

“Har ga Allah ba zan iya tunawa ba, saboda ba na kirgawa, amma na san suna da yawa. A ranar da a ka cafke ni, na kashe mutum uku. Lokacin da a ka tambaye dalilin da ya sa ya kashe su, sai ya ce, mai gidana ya bayyana min cewa, idan bai kashe wadanda a ka yi garkuwa da su, to zai kashe ni. “Duk lokacin da na ki kashe su, to ina cikin tsoro saboda na sabawa umurnin mai gidana, sannann kuma ni ma zai iya kashe ni,” in ji Haruna.

Ya cigaba da cewa, a cikin masu garkuwan, akwai malami wanda ya ke yi wa gawa sallah kamar yadda addinin Muslunci ta tanada. “Malamin zai musu addu’ar Allah ya ji kan su, sannan saii mu burne su a cikin rami.”

Ya bayyana cewa, ya yi aure har ma ya na da yara, matarshi ba ta san ya na aikata wannan mummuman sana’ar ba, saboda ya boye mata. Wanda a ke zargin ya bayyna cewa, inifom din sojoji da ya ke sakawa, mai gidansu ne ya kawo masa. Ya ce, akwai hannun ‘yan sanda a cikin lamarin. Ya kara da cewa, ya san cewa, abinda ya ke ba dai-dai ba ne, amma ya na tsoron fita daga  cikin su, domin idan ya fita, to za su kashe shi. Ya na mai cewa, idan a ka sake shi, to zai hada hannu da ‘yan sanda wajen cafko duk wani mai garkuwa da mutane, domin ya san hanyoyin da su ke bi wajen gudanar da wannan mummunar aikin.

Idan za a iya tunawa, ‘yan sanda sun taba gurfanar da Haruna a ranar 3 ga watan Yunin shekarar 2019. An samu nasarar cafke shi ne, bayan kaddamar da farmaki a kan masu garkuwa da mutane, ‘yan bindiga, bayayin shanu da kuma ‘yan fashi da makami. Lokacin da a ke gurfanar da su, wasu daga cikin wadanda a ke zargin sun bayyana cewa, su na safarar makamansu ne tun daga kasashen Libya, Burkina Faso, Benin  da kuma ta kasar Nijer.  An kwato sunkin harsashi guda 6000 na bindiga kirar AK-47, bindigogi kirarar AK-47 da dama da kuma kananan bindigogi da dama daga hannun wadanda a ke zargi. Wadanda a ke zargin sun bayyana cewa, sun sayar da wadannan makamai ga sauran masu garkuwa da mutane, ‘yan fashi da makamai da kuma sauran ‘yan ta’adda da ke cikin kasar nan.

Exit mobile version